NDDC: Za mu hukunta duk wadanda suka yi badakala a Neja – Buhari ya lashi takobi

NDDC: Za mu hukunta duk wadanda suka yi badakala a Neja – Buhari ya lashi takobi

  • Gwamnatin Tarayya za ta yi aiki da binciken da aka yi a kan hukumar NDDC
  • Shugaban kasa zai shiga kotu da duk wadanda suka wawuri dukiyar talakawa
  • Za a hukunta ‘yan siyasa da ‘yan kwangilar da suka yi badakala a Neja-Delta

Abuja - Gwamnatin tarayya tace za ta soma shirin shiga kotu domin a gurfanar da ‘yan siyasa, kamfanoni da ‘yan kwangilar da suka ci dukiyar NDDC.

The Nation ta rahoto shugaban kasa Muhammadu Buhari yana cewa za a hukunta wadanda aka samu da rashin gaskiya a binciken da aka yi wa hukumar.

Rahoton binciken NDDC ya shiga hannu

Mai girma Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne yayin da yake karbar rahoton wannan bincike da aka yi daga Ministan Neja-Delta, Godswill Akpabio.

Rahoton yace babban lauyan gwamnatin tarayya, kuma Ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami (SAN), ya karbi rahoton a madadin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke dan bindigan da ya sace daliban Kwalejin Noma na Afaka

Abubakar Malami (SAN) yake cewa gwamnatin Buhari ta damu da irin asarar da ake tafka wa a yankin Neja-Delta saboda watsi da kwangilolin da ake yi.

AGF yake cewa an ware wa hukumar cigaban Neja-Deltan Naira tiriliyan 6 daga 2001 zuwa yau, ba tare da an ga wani tasirin hakan a yanki mai arzikin mai ba.

'Yan Neja-Delta
Buhari da manyan Neja-Delta premiumtimesng.com
Asali: Twitter

Shawarar da aka ba gwamnati

Rahoton binciken da aka yi ya bada shawarar NDDC ta rika tsaya wa a kan kasafin kudin da aka yi mata, ta daina kirkiro wasu sababbin ayyuka na dabam.

Tabir Ahmed, wanda shi ne shugaban wadanda suka yi binciken na kwa-kwaf, ya bada shawarar a daina ba mutane kudi a hannu, sannan a rika sa ido sosai.

Haka zalika Tabir Ahmed ya kawo shawarar a samu tsarin da ake bi wajen bada kwangiloli a NDDC.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

Jaridar tace kungiyar matasa ta National Youth Council of Nigeria da wasu kungiyoyi masu zaman kansu, sun bukaci a dauki shawarar da aka ba gwamnati

Kashen-kashen Benuwai

Wasu ‘yan majalisa da aka zaba a jam'iyyar PDP a Benuwai suna mara wa Gwamna Samuel Ortom baya a rikicinsa da Minista ayyukan musamman, George Akume

‘Yan Majalisan sun yi taron-dangi, sun yi wa Sanata George Akume rubdugu. Sannan kuma kun ji cewa sun zargi jami'an tsaro da kashe-kashe da aka yi a Benuwai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel