‘Yan Majalisa sun fadi ainihin dalilin tsige su Nanono, sun ce ba don Allah aka yi ba

‘Yan Majalisa sun fadi ainihin dalilin tsige su Nanono, sun ce ba don Allah aka yi ba

  • Marasa rinjaye a Majalisa ba su gamsu da sauke Sabo Nanono da Saleh Mamman ba
  • Hon. Ndudi Elumelu yana ganin an sallami Ministocin ne domin kauda hankalin jama’a
  • Elumelu ya yi kira ga Gwamnatin Buhari ta inganta tsaro da tattalin arzikin Najeriya

AbujaDaily Trust tace marasa rinjaye a majalisar wakilan kasa, sun wofantar da sauke wasu Ministoci da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi.

‘Yan adawan majalisar tarayyar sun ce hakan ba komai ba ne face karkatar da hakalin mutane da yunkurin birne gazawar da gwamnatin APC ta yi kan mulki.

Da yake magana a ranar Alhamis, 2 ga watan Satumba, 2021, shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, Ndudi Elumelu (PDP, Delta) yace hakan duk a banza.

Jaridar ta rahoto Honarabul Elumelu yace mafi yawan ‘Yan Najeriya ba su rudu da cire Ministocin ba.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun jefa CBN, NNPC a matsala, ana zarginsu da sama da fadi duk shekara

Ndudi Elumelu yake cewa an sauke Ministocin ne a lokacin da tsare-tsaren da suka sa jama’a kuka da rashin gaskiya suka zama tambarin gwamnati mai-ci.

‘Dan majalisar ya yi kira ga Mai girma Muhammadu Buhari ya inganta tsaro da tattalin arziki, a maimakon ya buge da sauke wasu daga cikin ‘yan majalisarsa.

Ndudi Elumelu
Honarabul Ndudi Elumelu a Majalisa Hoto: www.today.ng
Asali: UGC

Abin da marasa rinjaye suka fada

A cewar ‘dan majalisar na jihar Delta, gaza wa, rashin iya mulki da son-kai suka jefa al’ummar Najeriya a cikin halin da ake ciki a karkashin jagorancin Buhari.

“A maimakon ya yi abin da bai da amfani da neman kawar da hankalin al’umma, marasa rinjaye suna kira ga shugaban kasa ya magance harkar tsaro da ya tabarbare, da matsin lambar tattalin arziki a sanadiyyar rashin iya mulki, kama-karya da mulkin wariyan da yake aiki a karkashin jagorancinsa.”

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisar PDP sun zargi Jami’an tsaro da hada-kai da ‘Yan bindiga a jihar Arewa

“Majalisar marasa rinjaye ta yi imani cewa shugabanci na bukatar tsayin-daka, nuna iya wa, da yi da gaske, da kuma gaskiya da buda ido a kowane mataki.”

Meyasa Buhari ya yi sallama?

Fadar Shugaban kasa ta yi karin haske a kan dalilin tsige Ministocin suna tsakar wa’adinsu. Femi Adesina yace an lura da tsadar kayan abinci da matsalar wuta.

Femi Adesina ya kuma bayyana abin da ya sa Abubakar Aliyu da Muhammad Mahmud suka maye guraben Saleh da Nanano kafin a nada wasu Ministocin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng