Nasara: Jami'an tsaron hadin guiwa sun ragargaji 'yan bindiga da suka kai farmaki Shinkafi, Zamfara

Nasara: Jami'an tsaron hadin guiwa sun ragargaji 'yan bindiga da suka kai farmaki Shinkafi, Zamfara

  • Rundunar ‘yan sanda ta musamman da sauran jami’an tsaro sun mayar da harin da ‘yan ta’adda suka kai garin Shinkafi a jihar Zamfara
  • Jami’in hulda da jama’an jihar na ‘yan sanda, SP Muhammad Shehu ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Juma’a a Gusau
  • A cewarsa, sun yi musayar wuta na tsawon sa’a daya, har suka samu nasarar raunata 1 daga cikin ‘yan ta’addan yayin da sauran suka tsere da raunuka

Shinkafi, Zamfara - Rundunar hukumar ‘yan sanda na musamman tare da hadakar sauran jami’an ta mayar da farmakin da daruruwan ‘yan bindiga suka kai garin Shinkafi, hedkwatan karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, an samu wannan bayanin ne a wata takarda ta ranar Juma’a wacce jami’in hulda da jama’a, SP Muhammad Shehu ya saki a Gusau.

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisar PDP sun zargi Jami’an tsaro da hada-kai da ‘Yan bindiga a jihar Arewa

Nasara: Jami'an tsaron hadin guiwa sun ragargaji 'yan bindiga da suka kai farmaki Shinkafi, Zamfara
Jami'an tsaron hadin guiwa sun ragargaji 'yan bindiga da suka kai farmaki Shinkafi, Zamfara. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Shehu ya ce ‘yan bindiga wadanda ‘yan sansanin shu’umin dan bindigan nan, Turji, sun yi musayar wuta da jami’an tsaron a Shinkafi don kariya ga lafiyar jama’a da dukiyoyinsu.

“Bayan kammala musayar wutar wacce aka yi sa’a daya ana yi, daya daga cikin ‘yan ta’addan ya samu munanan raunuka saboda alburusai, sannan sauran kuwa ta yuwu sun samu raunukan,” a cewar PPRO din.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba Elkanah, ya tura wasu jami’an tsaron zuwa yankin don su tallafa wa wadanda aka tura can idan wasu ‘yan ta’adda suka sake kai farmaki, Daily Nigerian ta wallafa.

Elkanah ya yaba da jajircewar jami’an tsaron a kan yadda suka zage damtse suka yaki ‘yan ta’addan kuma suka ci gaba da kulawa da rayuka da dukiyoyin jama’an jihar.

'Yan sanda sun bindige Buba Baromi, kasurgumin mai kai wa 'yan bindiga bayanai a Niger

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi luguden wuta, sun kashe ‘Yan bindiga rututu da su ka fake a jejin Zamfara

A wani labari na daban, jami'an rundunar yaki da 'yan bindiga ta 'yan sandan jihar Niger sun bindige gagararren mai kai wa 'yan bindiga bayanai, Buba Baromi. An sheke Baromi ne a wata maboyarsa da ke dajin Damba na jihar Niger, PRNigeria ta ruwaito.

PRNigeria ta tattaro cewa, wasu mafarautan yankin sun jagoranci 'yan sanda maboyar Baromi inda ya ke jinyar wani harbin bindiga da aka yi masa yayin wata arangama da yayi da jami'an tsaro a baya.

Wani jami'in sirri da aka yi aikin da shi, ya sanar da PRNigeria cewa, Baromi ba bayanai kadai yake kai wa 'yan bindiga ba, har jagorantarsu yake yi zuwa wurin da za su kai farmaki kuma su sace jama'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel