Sojojin sama sun yi luguden wuta, sun kashe ‘Yan bindiga rututu da su ka fake a jejin Zamfara
- Sojojin saman Najeriya sun kashe ‘Yan bindiga da yawa a dajin Shinkafi
- Barin wutan da jirgin yakin sojoji ya yi, ya kashe ‘yan bindiga kimanin 50
- Dakarun sojin sun hallaka yaran Kachalla Haru da ke boye a Gidan Rijiya
Zamfara - Wani jirgin yakin sojojin saman Najeriya, ya hallaka ‘yan bindiga rututu da ke cikin wata makaranta a karamar hukumar Shinkafi, Zamfara.
Jaridar Leadership ta fitar da rahoto cewa jirgin yakin ya kuma yi shawagi a sararin samaniya, ya kashe ‘yan bindiga a yankin Zangon Dammaka da Jajaye.
A wannan hari da aka kai a ranar Lahadi, 29 ga watan Agusta, 2021, dakarun sojojin saman kasar sun rugurguza mafakar Kachalla Haru da wasu yaransa.
Wani jami’in tsaro da yana cikin tawagar sojojin, ya shaida wa PRNigeria cewa sun yi nasara a duka hare-haren da suka kai a karshen makon da ya wuce.
Yadda abin ya faru
“A ranar 29 ga watan Agusta, 2021, da kimanin karfe 2:00 na rana, aka samu bayanin cewa ‘yan bindiga sama da 100 sun mamaye wata makaranta a kauyen Gidan Rijaya a garin Galadi, karamar hukumar Shinkafin jihar Zamfara.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Nan take jirgin yakin Alpha Jet da ke hannun Operation Hadarin Daji ya tashi, ya kai farmaki a yankin. A dalilin haka ya kashe tulin ‘yan bindiga, ya rugurguza makamansu.”
“Jirgin ya kuma yi barin wuta a tsaunukan Halilu Tubali a jejin Sububu. An ci nasara a duka wadannan hare-hare, ba tare da an yi wata asara ba face wani gini da aka rusa.”
Mutane nawa aka kashe?
PR Nigeria tace har yanzu babu tabbacin adadin ‘yan bindigan da suka mutu a wadannan hare-haren.
Ganin yawan baburan da aka rusa a kauyen na Gidan Rijiya, rahoton ya ce ana hasashen ‘yan bindiga fiye da 50 sun bakunci barzahu a karshen makon jiyan
An yi yunkurin tuntubar kakakin sojojin sama, Air Commodore Edward Gabkwet, amma ba a dace ba.
B/Haram: Amurka za ta taimaki Najeriya
Kun ji Jakadar Amurka, Mary Leonard ta ce gwamnatinsu ta shirya bada gudumuwa domin tona asirin wadanda ke taimaka wa 'yan Boko Haram a Najeriya.
Kyakkyawar alakar Najeriya da Amurka tana kara karfi a gwamnatin Joe Biden. Jakadar Amurkar ta ce Najeriya ba za ta zama kamar Afghanistan ba.
Asali: Legit.ng