Abin da ya sa Malaman Jami’a ba za su fara yajin-aiki a yau ba inji Shugaban ASUU

Abin da ya sa Malaman Jami’a ba za su fara yajin-aiki a yau ba inji Shugaban ASUU

  • Da alama cewa malaman jami’o’i ba za su shiga yajin-aiki a ranar Talata ba
  • A daren yau wa’adin da kungiyar ASUU ta ba Gwamnatin Tarayya zai cika
  • Shugaban ASUU na jami’ar UNILAG yace sai ASUU tayi zaman NEC tukuna

Lagos – Wani jami’in kungiyar ASUU yace malaman jami’a ba za su dauki matakin zuwa yajin aiki a ranar Talata, 31 ga watan Agusta, 2021 ba.

Jaridar Vanguard ta fitar da wannan rahoto a ranar Litinin, 30 ga watan Agusta, 2021.

Wani daga cikin ‘yan majalisar kolin NEC na ASUU, ya yi magana da Vanguard, inda ya bayyana cewa akwai matakai da ake bi kafin ayi yajin-aiki.

Dr. Dele Ashiru wanda shi ne shugaban reshen jami’ar Legas na UNILAG ya zanta da ‘yan jarida a ranar Litinin, yace wa’adin da suka bada yana nan.

Kara karanta wannan

Yajin-aiki: Yau Malaman Jami’a za su dauki matsaya inji Shugaban kungiyar ASUU

Shugaban kungiyar na ASUU na UNILAG ya ke cewa sun ba gwamnatin tarayya zuwa karshen watan nan na Agusta domin a biya masu bukatunsu.

“Eh mun ba gwamnatin tarayya zuwa karshen watan nan, ta cika mana wasu daga cikin bukatunmu.”

Jami'ar Nsukka
Jami'ar Tarayya ta Nsukka Hoto: xscholarship.com
Asali: UGC

Ba haka kurum ake soma yajin-aiki ba

“Amma ko da ba a cika mana bukatunmu a lokacin da muka bada ba, ba za mu fara yajin-aiki daga ranar ba.”
“Dalilin kuwa shi ne kungiyar ASUU ba ta mutum daya ba, kuma ba wani mutum guda yake da iko da ita ba.”
“A wajen taron NEC za a bayyana mataki na gaba da za a dauka. Yanzu haka ba a sa ranar yin zaman NEC ba.”

Me ASUU ta ke nema wajen gwamnati?

Dr. Ashiru yake cewa don haka har zuwa jiya, babu tabbacin malaman jami’o’in gwamnati za su shiga yajin-aiki, su daina koyar da ‘daliban jami’an.

Kara karanta wannan

Abin da tsohon Sojan Najeriya ya fada da ya tsokano DIA ta ke neman shi ruwa a jallo

Jami’in yace bukatun ASUU uku ne; a biya su alawus, a tura masu kudin gyara jami’o’i, sannan a dabbaka duk yarjejeniyar da aka yi a shekarun baya.

Gwamnati ta ba 'Yan ASUU hakuri

A jiya ne aka ji Ministan ilmi yayi bayanin abin da ya sa gwamnatin tarayya ta gagara cika wa kungiyar ASUU wasu daga cikin bukatun da aka nema.

Emeka Nwajiuba ya bukaci malaman jami’a su kara hakuri, kar su shiga yajin-aikin. Amma ASUU ta zargi hwamnatin tarayya da kokarin yaudararta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng