Yajin-aiki: Yau Malaman Jami’a za su dauki matsaya inji Shugaban kungiyar ASUU
- Ministan ilmi yayi bayanin abin da ya sa ta gagara cika wa kungiyar ASUU alkawari
- Emeka Nwajiuba ya bukaci malaman jami’a su kara hakuri, kar su shiga yajin-aiki
- Shugaban kungiyar ASUU na zargin Gwamnatin Tarayya da yi wa al’umma karya
Abuja - A ranar Litinin, 30 ga watan Agusta, 2021, gwamnatin tarayya ta bayyana abin da ya sa ba ta cika alkawuran da ta yi wa malaman jami’a ba.
Punch ta yi hira da karamin Ministan ilmi na kasa, Emeka Nwajiuba, wanda ya bayyana cewa bankin CBN na kokarin tura kudin habaka jami’o’i.
Amma kungiyar ASUU ta maida martani, tace Ministan na kokarin yaudarar al’umma ne kurum bayan gwamnatin tarayyar ta ki cika alkawarinta.
Hon. Emeka Nwajiuba ya shaida wa jaridar cewa suna kokari domin ganin wadannan kudi sun kai ga jami’o’i, ya yi kira ga ASUU su kara yin hakuri.
Da yake bayani a jiya, Nwajiuba yace za a cika duk wata yarjejeniya da aka yi da ASUU, ya kuma yi kira ga kungiyar su tuntubi wakilan gwamnati.
Gwamnati ba ta daukar wayar ASUU?
A jiya aka ji shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, yana kukan gwamnati ta saba alkawuran da ta yi, sannan ba ta amsa kiran malaman.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Me zai hana gwamnatin tarayya ta dauki wayar ku? An kira ni da boyayyar lamba na dauka, ina kuma ga wayar ASUU? Su wane suka tuntuba?"
Shugaban ASUU ya maida martani
Da aka tuntubi shugaban ASUU na kasa, Emmanuel Osodeke, yace ba da gaske gwamnati mai-ci ta ke yi ba, kuma babu abin da ya dame su da talaka.
“Ba na tunanin da gaske suke yi. Da sun damu da ‘dan talaka da ba zai iya zuwa makarantar kudi ba, da sun rubuto mana, sun ba mu hakuri.”
“CBN da ma’aikatar tarayya sun nuna mana kudin suna CBN, meya wahalar a turo mana su? Hakan na nufin takardun bogi aka nuna mana.”
Farfesa Osodeke yace za su cigaba da sauraron gwamnati kafin su dauki mataki na gaba a yau, yayin da wa’adin da suka bada yake cika an jima kadan.
Ba haka abin yake ba - FG
Kwanakin baya aka ji gwamnatin tarayya ta na cewa zargin da kungiyar ASUU ta ke yi na cewa ba ta cika alkawuran da ta dauka ba, ba gaskiya ba ne.
Tun a farkon Agusta, Ministan kwadago, an ji Dr. Chris Ngige yace gwamnati ta biya kudin habaka jami’o’i, ya rage wa CBN su tura wa makarantun.
Asali: Legit.ng