Shugaba Buhari Ya Kadamar da Shirin Samarwa Matasa 20,000 Aiki, Ya Fadi Yadda Za'a Nemi Aikin

Shugaba Buhari Ya Kadamar da Shirin Samarwa Matasa 20,000 Aiki, Ya Fadi Yadda Za'a Nemi Aikin

  • Shugaba Buhari ya kaddamar da sabon shirin 'Jubilee Fellows,' wanda zai samarwa matasa 20,000 ayyukan yi
  • Shugaban ya roki matasa su nemi damar shiga a dama da su a shirin, wanda ake tsammani zai shafe wata 12
  • A yau Talata, Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya kaddamar da shirin a fadarsa dake Abuja

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya roki matasan Najeriya su shiga sabon shirin "Jubilee Fellows Programme,' wanda zai samar wa masu kwalin digiri 20,000 aikin yi.

Shugaban ya faɗi haka ne yayin kaddamar da shirin a fadarsa dake babban birnin tarayya Abuja, ranar Talata.

Legit.ng Hausa ta gano cewa shirin zai ɗauki matasa waɗanda ba su haura shekara 30 a duniya ba, kuma zai kwashe watanni 12.

Shugaba Buhari a wurin kaddamarwa
Shugaba Buhari Ya Kadamar da Shirin Samar da Aiki Ga Masu Digiri 20,000, Ya Fadi Yadda Za'a Nemi Aikin Hoto: Buhari Sallau Fb fage
Asali: Facebook

Mai taimakawa shugaban ƙasa, Buhari Sallau, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa shirin zai samar wa matasan aikin yi a wasu ɓangarorin gwamnati da masu zaman kansu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari ya roki matasa su yi amfani da wannan dama

Da yake jawabi wajen kaddamar da shirin a Abuja, Shugaba Buhari yace:

"Muna da yakinin cewa shirin zai samar da damarmaki ga matasan da suka kammala digiri 20,000 cikin watanni 12."
"Muna fatan waɗanda zasu amfana ɗa shirin zasu yi amfani da damar da suka samu wajen yin abinda ya dace a watanni 12 da zasu shafe."
"Wannan shirin zai taimakawa matasan Najeriya su samu kwarewar aiki da manyan kungiyoyi domin gina goben su ta ɓangarori da dama da suka haɗa da fahasar zamani, kasuwanci, noma da kiwo da kuma ayyukan da suka shafi mu'amala da kudi."

Gwamnatin Buhari ta maida hankali wajen samar da ayyukan yi

Shugaban ƙasa yace gwamnatin ta maida hankai matuka wajen samar da ayyukan yi ga yan Najeriya a matsayin hanyar habbaka tattalin arziki.

A wani bidiyo da Buhari Sallau ya buga a shafinsa na facebook, Buhari yace:

"Ɗaya daga cikin kudirorin mu da muka fi baiwa muhimmanci shine samar da ayyukan yi ga yan Najeriya."
"Bayan an zaɓe mu a 2015, mun kirkiro da abubuwa da dama na samar wa yan Najeriya aikin yi.
"Mun ɗauki yan Najeriya 500,000 da suka kammala karatu a shirin mu na N-Power dake karkashin tsarin jin kai da walwala."

A wani labarin kuma Gwarazan Yan Sanda Sun Ceto Mutum 8 da Yan Bindiga Suka Sace a Zamfara

Rundunar yan sanda a jihar Zamfara ta samu nasarar ceto wasu mutum 8 da yan bindiga suka sace a Bungudu.

Kakakin yan sandan jihar, ASP Muhammad Shehu, yace an samu wannan nasarar ne cikin ruwan sanyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel