Gwarazan Yan Sanda Sun Ceto Mutum 8 da Yan Bindiga Suka Sace a Zamfara

Gwarazan Yan Sanda Sun Ceto Mutum 8 da Yan Bindiga Suka Sace a Zamfara

  • Rundunar yan sanda a jihar Zamfara ta samu nasarar ceto wasu mutum 8 da yan bindiga suka sace a Bungudu
  • Kakakin yan sandan jihar, ASP Muhammad Shehu, yace an samu wannan nasarar ne cikin ruwan sanyi
  • Ya kuma yi kira ga mazauna jihar su cigaba da baiwa yan sanda goyon baya domin dawo da zaman lafiya a faɗin jihar

Zamfara - Rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara ta ceto mutum 8 da yan bindiga suka sace a ƙaramar hukumar Bungudu, jihar Zamfara kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, ASP Muhammad Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Gusau.

A cewarsa yan bindiga sun yi awon gaba da mutanen zuwa sansanin su dake Kungurmi, amma jami'ai sun ceto su cikin ruwan sanyi.

Kara karanta wannan

Bayan shafe kwanaki 88, 'yan bindiga sun sako daliban Islamiyyar Tegina da suka sace

Yan sanda sun ceto mutum 8 a Zamfara
Gwarazan Yan Sanda Sun Ceto Mutum 8 da Yan Bindiga Suka Sace a Zamfara Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Sanarwar tace:

"A kokarin da rundunar yan sandan jihar Zamfara take yi na kare rayukan al'umma da dukiyoyinsu, ta samu nasarar ceto wasu mutum 8 da aka sace cikin ruwan sanyi."
"Ɓarayin sun sace mutanen ne a ranar 25 ga watan Agusta a Kangon Sabuwa, karamar hukumar Bungudu."
"Jami'an yan sanda sun tabbatar da an duba lafiyar mutanen da aka ceto, sannan suka binciko iyalansu, suka mika su garesu."

Zamu cigaba da kokarin kubutar da mutanen da aka sace

ASP Shehu ya bayyana cewa rundunar yan sanda zata cigaba da haɗa kai da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da ceto mutanen dake hannun yan bindiga, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Kakakin yan sandan ya kuma yi kira ga mazauna jihar su cigaba da tallafawa jami'an yan sanda da sauran hukumomin tsaro a kokarinsu na dawo da dawwamammen zaman lafiya a faɗin jihar ta Zamfara.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Sace Sakataren Hukumar Zaɓe a Jihar Nasarawa

A wani labarin kuma Babban Malamin Addinin Musulunci Ya Bada Tallafin Sama da Miliyan N4m a Gina Coci, Mutane Sun Magantu

Babban limamin ƙasar Ghana, Dr Osman Nuhu Sharubutu, ya baiwa kiristoci tallafin dala dubu 10 kwatankwacin sama da miliyan N4m domin gina babbar coci.

Sai dai lamarin ya jawo kace-nace tsakanin al'ummar musulmi a kasar, inda suka nuna rashin jin dadinsu bisa matakin da limamin ya ɗauka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel