Magidanta 2 Sun Bai Wa Hammata Iska Kan Budurwa, Sun Tarwatsa Motar Ɗaya

Magidanta 2 Sun Bai Wa Hammata Iska Kan Budurwa, Sun Tarwatsa Motar Ɗaya

  • Wasu maza masu aure guda biyu sun ta bai wa hammata iska a kan wata budurwa a Makurdi, babban birnin Binuwai
  • Kamar yadda wani Atsuwe Shadrack ya wallafa a shafinsa na Facebook, turnukun da ya balle tsakaninsu ya yi sanadin asarar wata mota
  • Ya wallafa hotunan motar da suka kwankwatsa inda ya ce da safiyar Talata, 31 ga watan Augusta lamarin ya faru a kusa da babbar kasuwar Makurdi

Makurdi, Jihar Benue - Wani turnuku fadan ibilisai ya barke tsakanin wasu maza guda biyu masu aure har suna kwankwatsa wata mota duk a kan wata mata a Makurdi, babban birnin jihar Binuwai, LIB ta ruwaito.

Kamar yadda wani Atsuwe Shadrack ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, inda har hotunan lalatacciyar motar ya sa, ya ce lamarin ya auku ne da safiyar Talata, 31 ga watan Augustan 2021 kusa da babbar kasuwar Makurdi.

Kara karanta wannan

Cike da tawakkali, Sanata Na'Allah ya magantu kan kisan babban ɗansa

Magidanta 2 sun bai wa hammata iska kan budurwa, sun tarwatsa motar 1 daga ciki
Magidanta 2 sun bai wa hammata iska kan budurwa, sun tarwatsa motar 1 daga ciki. Hoto daga Astuwe Shadrack
Asali: Facebook

A cewar sa, motar mallakin daya daga cikin mazan ce.

Sai dai wata Fanen Dzua ta ce matan mai motar guda biyu ne don haka ba ta tunanin zai iya dambe ta dalilin mace.

Wannan lamarin ya na aukuwa ne kusa da babbar kasuwar Makurdi. Maza biyu masu aure suna ta bai wa hammata iska a kan wata mata.
Amma har hakan ya yi sanadiyyar lalata wannan motar. Duba ki gani idan har motar mijin ki ce, yana nan ya ware a bakin hanya yana kwasar dambe,” kamar yadda ya wallafa.

Musulunci Ya Haramta: Ban Goyon Bayan Halasta Amfani Da Wiwi, Ƴan Majalisar Kano Ma Basu Goyon Baya, Ganduje

A wani labari na daban, Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano, a ranar Litinin ya nuna rashin jin dadinsa kan yunkurin da ake yi na hallasta amfani da ganyen wiwi a Nigeria, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kutsa gidan dan sanatan Kebbi a cikin gidansa, sun hallakashi

Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi na kasa, NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa (mai murabus) da manyan jami'an hukumar suka kai masa ziyarar ban girma a Kano.

A sanarwar da kakakin NDLEA, Mr Femi Babafemi ya fitar, ya ce gwamnan ya ce babu wani dan majalisar tarayya daga jiharsa da zai goyi bayan irin wannan yunkurin, LIB ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel