Cike da tawakkali, Sanata Na'Allah ya magantu kan kisan babban ɗansa

Cike da tawakkali, Sanata Na'Allah ya magantu kan kisan babban ɗansa

  • Sanata Bala Ibn Na'Allah, sanatan da miyagu suka sheke dan sa, matukin jirgin sama a Kaduna, ya bayyana tawakkalinsa
  • Kamar yadda ya bayyana a safiyar Litinin, ya ce yana fatan mutuwar dan sa Abdulkarim ta zamo silar shawo kan matsalar tsaro
  • Kamar yadda ya bayyana a safiyar Litinin, ya ce rayuwar dan sa abun alfaharinsa daidai take da ta kowanne dan Najeriya

Kaduna - Sanata Bala Ibn Na'Allah, wanda miyagu suka halaka babban dan shi Abdulkareem a gidan shi da ke Malali jihar Kaduna, ya ce rayuwar dan shi ba ta fi ta kowanne dan Najeriya ba.

A wata takarda da ya fitar a ranar Litinin, Na'Allah ya bayyana fatansa na cewa ta yuwu mutuwar dan sa ta taka babban rawa wurin shawo kan matsalar tsaron Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Garabasa: Matashi na neman budurwar da zata so shi, zai ba ta albashin N150k duk wata

Cike da tawakkali, Sanata Na'Allah ya magantu kan kisan babban ɗansa
Cike da tawakkali, Sanata Na'Allah ya magantu kan kisan babban ɗansa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Sanata Na'Allah wanda baya kasar Najeriya yayin da lamarin ya auku, ya ce wadanda suka kai wa dan sa farmaki ba dauke suke da bindigogi ba.

Sun samu damar shiga gidansa ne ta rufi kuma suka shake shi. A matsayin mu na dangin shi, za mu cigaba da kaunarsa ko bayan mutuwarsa saboda mutum ne nagari yayin da yake raye.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rayuwarsa ba ta fi ta wani dan Najeriya ba. A matsayin mu na danginsa, mun bar komai a hannun Allah wanda tuni muka fawwala masa komai domin ya bamu hakurin jure rashin Abdulkareem a tare da mu.
Ko daga kira, sakonni da kuma ziyarar da muke ta samu, mun godewa Allah da irin wannan kaunar da jin kai da ya nuna gare mu," yace.

Na'Allah, sanatan da ke wakiltar Kebbi ta kudu, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan lamurran sojin sama, ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Kwamishinan 'yan sanda ya ba da umarnin a binciko wadanda suka kashe dan sanata

Muna tabbatarwa da jama'a cewa mun matukar jin kaskanci ta yadda aka kashe shi, amma kuma mun saka tawakkali a lamarin.
Za mu cigaba da jajircewa tare da hakurin wannan rashin da muka yi na babban jakadan dangin mu da muke alfahari da shi. Muna fatan mutuwarsa za ta taka babbar rawa wurin shawo kan matsalar da kasar mu ke fuskanta.

Ya mika godiyarsa ga 'yan sanda da gwamnatin jihar Kaduna kan daukin da suka kai tare da fatan rahama ta har abada ga Abdulkareem.

Daily Trust ta ruwaito cewa, matukin jirgin mai shekaru 36 a duniya shi ne babban dan Na'Allah wanda aka ga gawarsa a gidansa da ke titin Umar Gwandu a Malali, daya daga cikin kasaitattun anguwannin Kaduna.

Buhari ya gana da shugaban NIS, ya bada sabon umarni kan iyakokin kasar nan

A wani labari na daban, shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, NIS, Muhammed Babandede, a ranar Juma'a ya yi bayani ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan ayyukan NIS na kokarin tsare iyakokin kasar nan.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kutsa gidan dan sanatan Kebbi a cikin gidansa, sun hallakashi

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, a yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati a karshen taron sirri da yayi da shuagaban kasa, Babandede ya ce NIS ta kirkiro da sabbin tsare-tsare domin duba yanayin shige da fice bakin haure a kasar nan ba bisa ka'ida ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel