'Yan ta'adda sun kutsa gidan dan sanatan Kebbi a cikin gidansa, sun hallakashi

'Yan ta'adda sun kutsa gidan dan sanatan Kebbi a cikin gidansa, sun hallakashi

  • Wasu 'yan ta'adda sun hallaka dan sanatan jihar Kebbi, Bala Na'Allah a cikin gidansa dake Kaduna
  • An ruwaito cewa, 'yan ta'addan sun kutsa cikin gidansa ne, inda suka daureshi suka kuma shake wuyanshi
  • Mahaifinsa ya Sanata Bala Na'Allah ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma sanar da ranar jana'iza

Kaduna - An gano gawar babban dan Sanata Bala Na Allah, Kyaftin Abdulkarim Bala Na Allah, a dakin kwanansa da ke Malali a jihar Kaduna.

Daily Trust ta tattaro cewa matukin jirgin mai shekaru 36, wanda ya yi aure kwanan nan, an daure shi kuma kana aka shake shi har ya mutu yayin da maharan suka tsere da motarsa ​​da kayayyakinsa.

Mai ba da shawara na musamman ga Sanata Na Allah, Garba Mohammed, yayin tabbatar da mummunan abin da ya faru, ya ce maharan sun samu shiga gidan ne ta rufin bayan gidansa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Gwamnan jihar Benue ne sanadiyyar mutuwar 'yan Najeriya da dama

Da Duminsa: An hallaka dan sanatan jihar Kebbi a cikinm gidansa
Abdulkarim Bala Na Allah | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Ya ce wani mai gadin makwabcinsa ya lura da cewa an bude kofar gidan marigayin tare da yin alama wanda ya kai ga gano gawar matukin.

An rawaito cewa Sanata Na Allah, wanda a halin yanzu baya Najeriya, yana da ‘ya’ya uku wadanda dukkansu matukan jirgi ne.

Da yake magana da wakilin Daily Trust, Mohammed ya ce za a yi sallar jana'izar marigayin a Yahaya Road yayin da za a bunne shi a makabartar Unguwan Sarki.

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna har yanzu ba ta mayar da martani kan kisan ba amma Mohammed ya shaida cewa an sanar da 'yan sanda kuma a halin yanzu suna wurin da kisan ya faru.

Bala Na’Allah yana wakiltar Kebbi ta Kudu a majalisar dattawa.

'Yan bindiga sun mamaye wani kauye a Kaduna, sun hallaka mutane biy

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan sanda sun damke mahaifiyar da ta garkame tare da hana dan ta abinci

'Yan bindiga sun hallaka mutane biyu a kauyen Makoro Iri dake karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna. A cewar wani rahoton tsaro, 'yan bindigar sun mamaye kauyen inda suka harbe mutane biyu da aka bayyana sunayensu da Gideon Mumini da Barnabas Ezra, Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi 29 ga watan Agusta.

A wani labarin kuma, rundunar Operation Safe Haven ta ceto matafiya uku daga hannun 'yan bindiga a hanyar Gidan Waya zuwa Godogodo a karamar hukumar Jema’a.

Bayan shafe kwanaki 88, 'yan bindiga sun sako daliban Islamiyyar Tegina da suka sace

A wani labarin, Sama da dalibai 70 'yan bindiaga suka sako na makarantar Islamiyya da ke garin Tegina wadanda aka yi garkuwa da su kwanaki 88 da suka gabata, PR Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Janar Abdulsalami: Ya kamata a sake zage dantse a nemo mafita ga tsaron kasar nan

Rahotanni a baya sun bayyana cewa, an sace daliban ne a harabar makarantar Islamiyyar dake Tegina a watan Yunin 2021.

Wata majiyar tsaro ta shaida wa jaridar PRNigeria cewa daliban na kan hanyarsu ta zuwa Minna akan hanyar Kagara daga Birnin Gwari.

An tsare daliban Islamiyyar na tsawon kwanaki 88 da awanni 11 gwargwadon lokacin da suka shafe a hannun 'yan bindigan kenan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel