Hotuna da bidiyon wankan 'Budan Kai' na Zahra Nasir Bayero, amaryar Yusuf Buhari

Hotuna da bidiyon wankan 'Budan Kai' na Zahra Nasir Bayero, amaryar Yusuf Buhari

  • A rana ta hudu a shagalin bikin dan shugaban kasa da 'yar sarkin Bichi, an yi budan kai jiya Asabar
  • An watsa wasu hotuna masu kawa yayin da amarya ta cancara ado domin shirin shagalin budan kai
  • Legit Hausa ta tattaro hotuna da bidiyo domin kar a bar mabiyanmu a baya cikin wannan babban biki

Abuja - A rana ta hudu a farin cikin bikin dan shugaban kasa, Yusuf Buhari da 'yar sarkin Bichi, Zahra Nasir Bayero, an yi shagalin budan kai jiya Asabar 21 ga watan Agusta.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne aka daura auren Yusuf Muhammadu Buhari da ga shugaban kasar da Najeriya da kuma Zahra Nasir Bayero 'yar sarkin Bichi.

Hotuna da bidiyon wankan 'Budan Kai' Zahra Nasir Bayero, amaryar Yusuf Buhari
Budan kai | Hoto: @tolabanks
Asali: Facebook

Ana ci gaba da shagalin biki, yayin da jiya Asabar ta kasance rana ta hudu a jerin jadawalin shagulgulan da ake gwangwajewa na bikin.

An yi budan kai jiya Asabar 21 ga watan Agusta, kuma Legit Hausa ta samo wasu daga cikin hotuna da kuma bidion shirin budan kai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalli hotunan da bidiyo:

Hotuna da bidiyon wankan 'Budan Kai' Zahra Nasir Bayero, amaryar Yusuf Buhari
Lokacin da ake cabawa amarya Zahra kwalliya | Hoto: @tolabanks
Asali: Instagram

Hotuna da bidiyon wankan 'Budan Kai' Zahra Nasir Bayero, amaryar Yusuf Buhari
Amarya bayan ta sha kwalliya | Hoto: @tolabanks
Asali: Instagram

Hotuna da bidiyon wankan 'Budan Kai' Zahra Nasir Bayero, amaryar Yusuf Buhari
Yayin da amarya ta iso gidansu ango | Hoto: @tolabanks
Asali: Instagram

Kalli bidiyo

Hotunan Aisha Buhari lokacin da take jiran isowar amaryar dan ta Yusuf Buhari

Kafin wannan budan kai, uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta watsa wasu hotunan manyan mutane da kawayenta da ke jiran karbar surukar ta, Zahra Nasir Bayero.

Aisha Buhari, da watsa hotunan a shafinta na Instagram ranar Asabar 21 ga watan Agusta ta ce:

"An shirya komai don maraba da karbar sabuwar 'yarmu cikin dangi."

An gan manyan iyayen biki, ciki har da uwargidan mataimakin shugaban kasa, Dolapo Osinbajo, Madame Fatoumatta Barrow da wasu mata su masu fada a ji.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel