Hotunan Aisha Buhari lokacin da take jiran isowar amaryar dan ta Yusuf Buhari

Hotunan Aisha Buhari lokacin da take jiran isowar amaryar dan ta Yusuf Buhari

  • Uwar gidan shugaban kasa a jiya ta yi zaman jiran karbar surukarta a fadar shugaban kasa
  • Rahoto ya bayyana yadda kawayen uwar gidan shugaba Buhari, Aisha ta zauna domin karbar surukarta
  • Legit Hausa ta samo hotunan lokacin da jiga-jigan matan Najeriya ke tare da Aisha Buhari a zaman jiran

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta watsa wasu hotunan manyan mutane da kawayenta da ke jiran karbar surukar ta, Zahra Nasir Bayero.

Aisha Buhari, da watsa hotunan a shafinta na Instagram ranar Asabar 21 ga watan Agusta ta ce:

"An shirya komai don maraba da karbar sabuwar 'yarmu cikin dangi."

An gan manyan iyayen biki, ciki har da uwargidan mataimakin shugaban kasa, Dolapo Osinbajo, Madame Fatoumatta Barrow da wasu mata su masu fada a ji.

Kara karanta wannan

Hotuna da bidiyoyin kasaitacciyar liyafar cin abinci dare ta bayan daurin auren Yusuf da Zahra

An daura auren Yusuf Muhammadu Buhari da Zahra Nasiru Bayero, ranar Juma'ar da ta gabata, bikin da ya samu sanya albarka da halartar manya daga sassan daban-daban na Najeriya da ma duniya.

Hotunan lokacin da uwar ango Aisha Buhari ke jiran isowar amaryar dan ta Yusuf
Uwar gidan shugaban kasa da kawayenta | Hoto: @aishabuhari
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalli hotunan jiran karbar amarya:

Hotuna da bidiyoyin kasaitacciyar liyafar cin abinci dare ta bayan daurin auren Yusuf da Zahra

Allah ya nufa, alkawarin masoya ya cika. A jiya ne Juma'a ne aka daura auren da namiji daya tilo na shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Muhammadu Buhari da Gimbiya Zahra Nasir Bayero, diya ga sarkin Bichi, Mai martaba Alhaji Nasir Ado Bayero.

Auren da minsitan sadarwa, Ali Isah Pantami ya daura kan sadaki naira dubu dari biyar a masarautar Bichi, ya kwashi shugabanni, 'yan siyasa, 'yan kasuwa na kasar nan da ketare.

Jim kadan bayan daurin auren, jama'a sun dinga tururuwa inda suka garzaya wurin liyafar cin abincin dare da aka hada domin ango Yusuf Buhari da matarsa, Gimbiya Zahra Nasir Bayero.

Kara karanta wannan

Daurin auren Yusuf Buhari: Jiragen Alfarma fiye 25 ne suka dira a Kano, Ƴan Nigeria sunyi martani

Tabbas wurin ya matukar daukar kala ganin yadda 'ya'yan gwamnoni, ministoci, masu mulki, 'yan kasuwa, har da 'yan fim suka yi dafifi domin taya sabbin ma'auratan murna.

Bidiyoyi: An daura auren Yusuf Buhari da Zahra Bayero kan sadaki N500,000

A wani labarin, Allah ya yadda, alkawari kuma ya cika. An daura auren Yusuf Muhammadu Buhari, da daya tilo namiji na shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gimbiya Zahra Nasir Bayero, diyar mai martaba Sarki Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero.

Babu shakka garin Bichi dake jihar Kano ya cika dankam da jiga-jigai na fadin kasar nan har da kasashen ketare, wadanda suka dinga tururuwar zuwa shaida daurin auren.

A hotuna da bidiyoyin da Legit.ng ta tattaro muku, an hango manyan 'yan siyasa da suka hada da gwamnoni, ministoci da fitattun 'yan siyasar kasar nan.

Ba a kasar nan kadai, Shugaban kasar Jamhuriyar Nijar, Shugaba Bazoum Mohammed ya halarci wannan gagarumin daurin auren.

Kara karanta wannan

Wani dattijo dan shekara 70 ya yiwa dan Shugaba Buhari tayin auren diyarsa a mata ta biyu, an yi cece-kuce

Asali: Legit.ng

Online view pixel