Hoton yadda Atiku da Buhari suka yi watsi da banbancin siyasa a Bichi
- Tun kafin zaben shekarar 2019 rabon da a ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a tare da juna
- Duk da dai Atiku, ya tsaya takarar shugaban kasa a shekar karkashin jam’iyyar PDP kuma ya sha kaye, hakan yasa ya zargi magudi har ya kai kara kotu
- A ranar Juma’a, daurin auren dan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf da diyar Sarkin Bichi, Zahra sai gasu sun ajiye siyasa suna gaisuwa cike da murmushi
Bichi, Kano - Karshen gaisuwar da aka ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abukar suna yi a fili shine tun kafin zaben 2019.
Daily Trust ta ruwaito cewa, dama Atiku ya tsaya takara ne a karkashin jam’iyyar PDP, sai dai ya sha mugun kaye bayan an sanar da Muhammadu Buhari a matsayin wanda yayi nasara.

Asali: Facebook
A lokacin Atiku ya harzuka har ya maka kara zuwa kotu wacce shari'ar har ta kai kotun koli domin yana zargin an yi magudi a zaben.
Sai ga shi a ranar Juma’a ana tsaka da daura auren Yusuf, dan Muhammadu Buhari da diyar sarkin Bichi, Zahra, sun ajiye siyasa a gefe.
Anga Atiku da Shugaban kasa suna gaisawa cikin farinciki da annashuwa, Daily Trust ta ruwaito.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya halarci daurin auren Yusuf Muhammadu Buhari da Gimbiya Zahra Nasir Bayero.
A tsaya daga haka ba, an ga fitaccen dan siyasan kuma mai sarauta a Adamawan suna gaisuwa irin ta korona cike da murmushi da annashuwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Yaki da ta'addanci: Janar Irabor na neman taimakon hafsoshin soji da suka yi murabus
A wani labari na daban, a ranar Laraba, Shugaban ma'aikatan tsaro na Najeriya, Janar Leo Irabor, ya ce sojoji suna bukatar samun dabaru da kwarin guiwa daga sojojin da suka yi murabus don cigaban kasa.
Daily Trust ta ruwaito cewa, ya yi wannan furucin ne yayin jawabi a wani taron karawa juna sani na manyan sojojin Najeriya na yankin arewa ta tsakiya da suka yi a Makurdi.
A cewarsa, sojoji suna da damar da zasu kawo karshen duk wasu rashin tsaro da suke addabar kasa, amma ya bukaci sojoji masu murabus da kada su sare ko su yi tunanin sun fita daga cikin masu baiwa kasa tsaro, hasalima su amince da cewa suna da ruwa da tsaki a harkar tsaro.
Asali: Legit.ng