Yaki da ta'addanci: Janar Irabor na neman taimakon hafsoshin soji da suka yi murabus

Yaki da ta'addanci: Janar Irabor na neman taimakon hafsoshin soji da suka yi murabus

  • Shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Leo Irabor, ya ce akwai bukatar sojoji su nemi dabaru da kwarin guiwa daga sojojin da suka yi murabus don samar da zaman lafiya a kasa
  • Ya yi wannan furucin ne yayin jawabi a wani taro na manyan sojoji da suka yi murabus na yankin arewa ta tsakiya da aka yi a Makurdi
  • Irabor ya bukaci sojojin da suka yi ritaya da kada su dauka cewa sun kammala ayyukansu, face suma suna da rawar takawa a harkar tsaro

Makurdi, Benue - A ranar Laraba, Shugaban ma'aikatan tsaro na Najeriya, Janar Leo Irabor, ya ce sojoji suna bukatar samun dabaru da kwarin guiwa daga sojojin da suka yi murabus don cigaban kasa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya yi wannan furucin ne yayin jawabi a wani taron karawa juna sani na manyan sojojin Najeriya na yankin arewa ta tsakiya da suka yi a Makurdi.

Kara karanta wannan

Kokwanto kan tubabbun Boko Haram: Akwai lauje cikin nadi ko tuban mazuru ne?

Yaki da ta'addanci: Janar Irabor na neman taimakon hafsoshin soji da suka yi murabus
Yaki da ta'addanci: Janar Irabor na neman taimakon hafsoshin soji da suka yi murabus. Hoto daga thecable.ng
Asali: Facebook

Sojoji suna da wuka da nama na kawo karshen rashin tsaro

A cewarsa, sojoji suna da damar da zasu kawo karshen duk wasu rashin tsaro da suke addabar kasa, amma ya bukaci sojoji masu murabus da kada su sare ko su yi tunanin sun fita daga cikin masu baiwa kasa tsaro, hasalima su amince da cewa suna da ruwa da tsaki a harkar tsaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Irabor:

Don tabbatar da zaman lafiya a kasar nan, muna bukatar neman dabaru daga manyan sojoji wadanda suka yi murabus. Saboda sun yi aikin nan kuma suna da dabaru da masaniya akan yadda ake shawo kan matsalar tsaro.
Matsawar ka taba zama soja, har abada kai soja ne ko da kana aiki ko kayi murabus. Babban burin kasar nan shine samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da natsuwa kuma mun yi rantsuwa akan tabbatar da hakan kuma za mu yi iyakar kokarinmu, a cewarsa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari, Osinbajo da shugabannin tsaro na ganawa a Aso Rock

A jawabin CDCIMIC, Rear Admiral Frederick Ugo, ya bayyana muhimmancin tattunawa tsakanin sojoji masu murabus da masu aiki a halin da kasa ta tsinci kanta, Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa:

Mun samu horarwa mai yawa, ilimi da dabaru na musamman a hannunsu. Suna da salon gano hanyoyin shawo kan matsalar tsaro saboda tunaninsu da namu zai banbanta.
Wajibi ne mu hada karfi da karfe wurin shawo kan matsalar rashin tsaro.

Dama AOC, AVM Idi Lubo, a nashi jawabin ya bayyana imaninsa akan tabbas akwai wani lamari mai kyau da zai zo nan kusa.

Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong

A wani labari na daban, Simon Lalong, gwamnan jihar Filato ya bayar da umarnin damke duk wanda yayi gaggawar zuwa belin wandanda aka kama ana zargin suna da hannu a kan farmakin jiharsa.

Gwamnan jihar ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wani taron gaggawa da yayi da manyan jami’an tsaro a Jos, Thecable.ng ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hawaye sun kwaranya yayin da ‘yan bindiga suka harbe sojoji 7 har lahira a Katsina

Kamar yadda NAN ta ruwaito, an yi taron na musamman ne a ranar 14 ga watan Augusta akan harin da aka kai karamar hukumar Bassa, Jos ta kudu, Barikin Ladi da Riyom.

Asali: Legit.ng

Online view pixel