Daurin auren Yusuf Buhari: Yemi Osinbajo ya dira garin Kano

Daurin auren Yusuf Buhari: Yemi Osinbajo ya dira garin Kano

  • Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya dira a jihar Kano domin daurin auren dan shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Osinbajo ya samu tarba ne daga gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, suna kuma jiran saukar Shugaba Buhari wanda zai taso daga Yola
  • Za a dai kulla aure tsakanin Yusuf Buhari da 'yar sarkin Buchi a yau Juma'a, 20 ga watan Agusta

Bichi, jihar Kano - Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya isa filin jirgin sama na Aminu Kano da ke jihar Kano domin daurin auren dan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Yusuf, da daya tilo da Shugaba Buhari ya mallaka, zai auri Zahra, diyar Alhaji Nasir Bayero, Sarkin Bichi.

Daurin auren Yusuf Buhari: Yemi Osinbajo ya dira garin Kano
Yemi Osinbajo ya dira garin Kano don halartan daurin auren Yusuf Buhari Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano ne ya tarbi mataimakin shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Siyasa a gefe: Hotunan Fani-Kayode yayin da ya shiga sahun manyan ‘yan APC don halartan daurin auren dan Buhari

Shugabannin biyu tare da wasu manyan jami'an gwamnati suna jiran shugaban kasa, wanda ake sa ran zai tashi daga Yola, babban birnin jihar Adamawa, kowane lokaci daga yanzu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaba Buhari ya dira birnin Yola don gaisuwar ta'aziyyar Ahmad Joda

A gefe guda, mun kawo cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Yola, jihar Adamawa a ranar Juma'a, 20 ga Agusta, domin gaisuwar ta'aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Ahmed Joda.

Buhari ya dira ne misalin karfe 10 na safe tare da tawagarsa. Hadimin Buhari na gidajen rediyo da talabijin, Buhari Sallau, ya bayyana haka.

Dirarsa ke da wuya, Buhari ya garzaya fadar Lamidon Adamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng