Kanwar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi Ta Rigamu Gidan Gaskiya

Kanwar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi Ta Rigamu Gidan Gaskiya

  • Yar uwa ga kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi ta rigamu gidan gaskiya ranar Alhamis
  • Matar mai suna Husaina Umaru, ta rasu tana da shekara 50 a duniya, ta bar ɗa ɗaya
  • Mai magana da yawun kakakin majalisar, Abdul Burra, shine ya sanar da rasuwar da yammacin Alhamis

Bauchi - Yar uwar kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Suleiman, wacce take binsa ta rigamu gidan gaskiya, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Marigayya mai suna, Hussaina Umaru, yar kimanin shekara 50 ra rasu ne ranar Alhamis bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun kakakin majalisar, Abdul Burra, ya fitar ranar Alhamis.

Kanwar kakakin majalisar Bauchi ta rasu
Kanwar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi Ta Rigamu Gidan Gaskiya Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ta rasu ta bar ɗa guda ɗaya

Ya bayyana cewa marigayya Hussaina ta rasu ta bar ɗa guda ɗaya, kuma za'a yi jana'izar ta kamar yadda addinin musulunci ya tanazar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: INEC Ta Canza Dan Takarar APGA, Ta Cire Jam'iyyar PDP Daga Zaben Gwamnan Anambra 2021

Burra, a cikin sanarwar yace:

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Cikin takaici kuma da mika lamarinmu ga Allah, muna sanar da rasuwar kanwar kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Honorabul Abubakar Y Suleiman, mai suna Hussaina Umaru Bandirawo."
"Ta rasu da yammacin ranar Alhamis 19 ga watan Agusta bayan fama da gajeriyar rashin lafiya."
"Za'a gudanar da jana'izarta yau da yamma a babban masallacin Jumu'a dake Gwallaga cikin garin Bauchi."

A wani labarin kuma INEC Canza Dan Takarar APGA, Ta Cire Jam'iyyar PDP Daga Zaben Gwamnan Anambra 2021

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta canza sunan Michael Umeoji, zuwa Chukwuma Soludo, a matsayin ɗan takarar gwamnan Anambra karkashin jam'iyyar APGA.

Hakazalika, INEC ba ta sanya jam'iyyar PDP ba a jerin waɗanda ta tantance zasu fafata a zaɓen gwamnan dake tafe ranar 6 ga watan Nuwamba 2021.

Kara karanta wannan

Hotunan ziyarar Shehu Dahiru Usman Bauchi zuwa fadar shugaba Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel