Hotunan ziyarar Shehu Dahiru Usman Bauchi zuwa fadar shugaba Buhari
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da Sheikh Dahiru Bauchi a fadar shugaban kasa
- Sheikh Dahiru Bauchi ya samu rakiyar ministan sadarwa, Sheikh Dr Isa Ali Ibrahim Pantami
- Legit Hausa ta samo hotunan ganawar tasu, sannan ta kawo muku rahoton ganawar tasu
Abuja - Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammdu Buhari (mai ritaya), ya karbi bakuncin jagoran darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi a fadar gwamnati da ke Abuja ranar Alhamis 19 ga watan Agusta, 2021.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ne ya watsa hotunan ganawar tasu a kafar Facebook.
Ya rubuta cewa:
"Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Shahararren Malamin Addinin Musulunci kuma Jagoran Darikar Tijjaniyya Sheikh Dahiru Usman Bauchi a gidan gwamnati a ranar 19 ga Aug 2021."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sheikh ya samu rakiyar Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Sheikh Dr Isa Pantami.
Duba hotunan
Buhari ya tausawa wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa barna, ya ce zai taimaka musu
A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna juyayi ga iyalai da sauran wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su sakamakon ci gaba da ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a makwannin da suka gabata, Daily Nigerian ta ruwaito.
Wannan lamarin da ya shafi dubban mutane a jahohi 32 na Najeriya, ya haifar da asarar gidaje, gonaki, rayuka da rushewar rayuwa ta yau da kullun.
Shugaban, wanda ya koma aiki a ranar Laraba bayan kebewa na kwanaki biyar bayan balaguro zuwa Landan, ya nuna damuwa kan halin da ake ciki, in ji News Diary.
Asali: Legit.ng