Da Duminsa: INEC Canza Dan Takarar APGA, Ta Cire Jam'iyyar PDP Daga Zaben Gwamnan Anambra 2021

Da Duminsa: INEC Canza Dan Takarar APGA, Ta Cire Jam'iyyar PDP Daga Zaben Gwamnan Anambra 2021

  • Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sake fitar da sunayen yan takarar gwamna a zaɓen Anambra dake tafe
  • Har yanzun dai INEC bata sanya sunan ɗan takarar PDP ba a cikin waɗanda zasu fafata a zaɓen
  • INEC ta bayyana cewa zata fitar da sunayen yan takara na karshe ranar 7 ga watan Oktoba

Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta canza sunan Michael Umeoji, zuwa Chukwuma Soludo, a matsayin ɗan takarar gwamnan Anambra karkashin jam'iyyar APGA.

Hakazalika, INEC ba ta sanya jam'iyyar PDP ba a jerin waɗanda ta tantance zasu fafata a zaɓen gwamnan dake tafe ranar 6 ga watan Nuwamba 2021, kamar yadda punch ta ruwaito

Kwamishinan INEC kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai, Festus Okoye, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja.

INEC ta sake fitar da jerin yan takarar gwamnan Anambra
Da Duminsa: INEC Canza Dan Takarar APGA, Ta Cire Jam'iyyar PDP Daga Zaben Gwamnan Anambra 2021 Hoto: vangauardngr.com
Asali: UGC

Kwamishinan yace:

"INEC ta zauna yau 19 ga watan Agusta 2021, kuma an tattauna abubuwa da dama, wanda ya haɗa da tsayar da yan takara a zaɓen gwamnan Anambra dake tafe ranar 6 ga watan Nuwamba."
"Jadawali da kuma tsarin ayyukan zaɓen da hukumar ta fitar ranar 18 ga watan Janairu, ya bada damar cirewa da maye ɗan takarar jam'iyya bisa dokar sashi na 35 ta kundin dokokin zaɓe."
"INEC ta yi amfani da hukuncin kotun ɗaukaka kara ta Kano, wanda ya soke hukuncin babbar kotun Jigawa kan shugabancin jam'iyyar APGA da kuma ɗan takararta a zaɓen gwamnan Anambra."

Yaushe INEC zata fitar da sunayen yan takara na karshe?

INEC Ta bayyana cewa a ranar 7 ga watan Octoba zata fitar sunayen yan takarar jam'iyyu na karshe, waɗanda zasu fafata a zaɓen gwamna ranar 6 ga watan Nuwamba.

Hukumar tace wannan duk yana cikin jadawalin yadda ayyukan zaɓen zai gudana wanda ta fitar tun a baya.

A wani labarin kuma Hukumar EFCC Ta Yi Ram da Tsohon Gwamnan Abia a Filim Jirgi, Ta Tsare Shi Tare da Dansa

Tsohon gwamnan, wanda ya jima a jerin sunayen waɗanda EFCC ke bincike a kansu, ya shiga hannu ne a filin jirgin Nnamdi Azikwe, Abuja da misalin karfe 10:00 na safe.

Yanzun haka yana tsare tare da ɗansa, Chinedu, kakakin majalisar dokokin jihar Abia na yanzu, wanda yazo bin ba'asi bayan gano an kame mahaifinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel