Gwamnan Zamfara ya ba Jihohi shawarar yadda za ayi maganin ta'adin ‘Yan bindiga cikin sauki

Gwamnan Zamfara ya ba Jihohi shawarar yadda za ayi maganin ta'adin ‘Yan bindiga cikin sauki

  • Gwamna Bello Matawalle yana bada shawarar a rungumi yin sulhu da ‘Yan bindiga
  • Gwamnan yace hakan ya yi masa amfani wajen kawo zaman lafiya a jihar Zamfara
  • Bello Matawalle ya yi kira ga Gwamnoni su dauki salon da ya dauka a gwamnatinsa

Zamfara - Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce jihohin Najeriya su dauki matakin sulhu da lalama domin a yaki ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro.

A ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta, 2021, The Cable ta rahoto Gwamna Bello Matawalle yana cewa sulhu da aka yi da ‘yan bindiga ya kawo masu zaman lafiya.

Da yake magana da hukumar dillacin labarai na kasa, gwamnan jihar Zamfara ya bada shawarar ayi koyi da matakin da ya dauka wajen tsare rayuka da dukiyoyi.

Mu gudu tare, mu tsira tare - Matawalle

Kara karanta wannan

Kwamishinan Neja da aka sako ya bayyana wadanda suka sace shi

“Kamar yadda na ambata a baya, sha’anin rashin tsaro ba matsalar wasu rukunin mutane kadai ba ce, aikinmu ne mu duka ne.”
“Ko kai jami’in tsaro ne, ko mazaunin gari ko gama-gari, muhimmin abu shi ne, duk mu hadu, mu dauka wannan matsalarmu ce, mu yi kokarin shawo kanta.”
“Bayan na zama gwamnan jihar Zamfara, na san cewa a kwanakin 100 na farko da na yi, mun ci nasarorin da ba a iya samu a shekaru shida da suka wuce ba.”

Gwamnan Zamfara
Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle Hoto: dgovscoops.com
Asali: UGC

Yadda Matawalle ya yi a jihar Zamfara

“Mun cin ma wannan nasara ne saboda na kira kowa, na zauna da shi. Mun tattauna da masu ruwa da tsaki; ‘yan siyasa, sarakuna, shugabanni da jami’an tsaro.”
“Muka hada karfi da karfe, shiyasa muka kawo maganar ayi zaman sulhu da lalama da ‘yan bindiga, kuma hakan ya kawo mana nasarori sosai a jihar (Zamfara).”

Kara karanta wannan

Ni fa sulhu kawai naje yi: Tsohon gwamna Bindow ya kare kansa kan zaman sukar Buhari

“Kowace jiha tana bukatar ta dauki irin wannan tsari na samar kwanciyar hankali. Idan muka hadu, muka dauki matsaya daya, na yi imani zai yi mana amfani.”

Jihohin yankin Arewa suna fama da ta’adin ‘yan bindiga da suke kashe jama’a da garkuwa da mutane.

Sanata Ali Ndume ya gargadi jami'an tsaro a kan yadda su ke tarairayar tubabban 'yan ta'adda, ya ce a binciki Mayakan Boko Haram da suka sare, suhka ajiye kayan yaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel