Ni fa sulhu kawai naje yi: Tsohon gwamna Bindow ya kare kansa kan zaman sukar Buhari

Ni fa sulhu kawai naje yi: Tsohon gwamna Bindow ya kare kansa kan zaman sukar Buhari

  • Tsohon gwamnan Adamawa ya saki jawabi kan zaman da yayi da wasu jigogin APC
  • A zaman, an ji yadda wasu suka ce gwanda Buhari ya mutu a huta
  • Sun ce Buhari babu abinda ya tsinanawa jihar Adamawa tun da ya hau mulki

Biyo bayan kalaman jama'a kan zaman da jigogin APC suka yi idan akayi kalaman suka ga shugaba Muhammadu Buhari, tsohon gwamnan Adamawa, Jibrilla Bindow, ya kare kansa.

Bindow a jawabin da ya saki ta hannun mai magana da yawunsa, Sadiq Abdullateef, Bindow yace ya halarci taron ne matsayin mai sulhu tsakanin bangarorim jigogin APC a Yola ta kudu biyu.

Ya ce ba shi ya kira taron ba, kawai gayyatarsa akayi, rahoton TheNation.

Jawabin yace:

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya fadi abinda zai hana mutanen kudu maso gabas shugabanci a 2023

"Ni, Senata Muhammad Umar Jibrilla Bindow ne mataimakin shugaban kwamitin sulhu na APC a Arewa maso gabas, kuma a cikin yin aikin da jam'iyya ta sa ni, an gayyaceni ganawa da wasu yan jam'iyya da suke rikici."
"Na halarci taron ne don sulhunta bangarorin biyu kan zaben fidda gwani. Sabanin rahotannin dake cewa na gana da bangare daya."

Ba zai yiwu ina wajen a so Buhari ya mutu ba, Bindow

Bindow yace da kyar suka sulhunta bangarorin biyu saboda na caba rikici a zaman shiyasa yayi mamaki da aka hadashi da lamarin sukan Buhari.

Yace: "Duk wanda ya san ni ya san an yi min tarbiyya mai kyau ba babu yadda zan zauna a waje ana kira ga mutuwar wasu, ballanatana Shugaba Muhammadu Buhari, wanda kaman mahaifi ne gareni."

Kara karanta wannan

Yahaya Bello ne matashin dan takarar da zai iya gyara Najeriya, in ji wani sanatan Kogi

Tsohon gwamna Bindow ya kare kansa kan zaman sukar Buhari
Ni fa sulhu kawai naje yi: Tsohon gwamna Bindow ya kare kansa kan zaman sukar Buhari Hoto: Bindow
Asali: Facebook

Da so samu ne, da Korona ta kashe Buhari mun huta: Shugaban APC a Yola

Shugaban rikon kwaryan jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a karamar hukumar Yola ta kudu, Sulaiman Adamu, ya caccaki shugaba Muhammadu Buhari, DailyNigerian ta ruwaito.

Adamu yace da so samu ne, da cutar Korona ta hallaka Buhari mataimakinsa Yemi Osinbajo ya hau kujerarsa.

A cewar majiyoyi, Jigon APCn ya bayyana hakan ne a ganawar wasu manyan masu ruwa da tsaki a jihar, ciki har da tsohon gwamnan Adamawa, Muhammadu Bindow da tsohon Kakakin majalisar jihar Adamawa, Kabiru Mijinyawa.

DSS ta gayyaci Bindow amsa tamayoyi

Jibrilla Bindow ya sha tarin tambayoyi akan wani taron juyawa Buhari baya da ya halarta tare da wasu manyan ‘yan jam’iyyar APC guda 5.

A ranar Laraba, 11 ga watan Augusta ne tsohon gwamnan ya sha tambayoyin a gaban hukumar tamkar tamabayoyin kurar hali.

Kara karanta wannan

Da so samu ne, da Korona ta kashe Buhari mun huta: Shugaban APC a Yola

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng