Lauyoyin Arewa 31 sun lashi takobin tsayawa Abba Kyari a kotu kyauta

Lauyoyin Arewa 31 sun lashi takobin tsayawa Abba Kyari a kotu kyauta

  • Akalla lauyoyi talatin da daya daga Arewacin Najeriya sun yanke shawaran kare DCP Abba Kyari a kotu
  • Lauyoyin sun yi hakan ne a matsayin amsa kiran gamayyar kungiyoyin arewa na karewa Abba Kyari hakkokinsa
  • Barista Bappah Salisu, a madadin lauyoyin ya bayyana cewa kyauta zasu yi

Abuja - Wani rahoton Vanguard ya nuna cewa akalla lauyoyin Arewacin Najeriya 31 sun alanta niyyar tsayawa mataimakin kwamishanan yan sanda Abba Kyari a kotu.

Lauyoyin sun yanke shawaran kare jami'in dan sandan ne bisa ga kiran gamayyar kungiyoyin Arewa inda ta bukaci a kare hakkokin Kyari.

Barista Bappah Salisu wanda ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a Abuja ranar Laraba, 11 ga Agusta ya ce zasu kare Abba Kyari kyauta, ThisDay ta kara.

Salisu wanda yayi magana a madadin lauyoyin yace an zabesu daga jihohin Arewa daban-daban, kuma akwai kura-kurai a bukatar da FBI tayi na a turo mata Abba Kyari.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya taya Musulmai murnar shiga sabuwar shekara

Lauyoyin Arewa 31 sun lashi takobin tsayawa Abba Kyari a kotu kyauta
Lauyoyin Arewa 31 sun lashi takobin tsayawa Abba Kyari a kotu kyauta Hoto: Abba Kyari
Asali: UGC

Abba Kyari ya sake gurfana gaban kwamitin bincike, an kwashe sa'a 4 yana shan tambayoyi

Abba Kyari, ya sha tambayoyi na sa'o'i hudu yayinda ya sake gurfana gaban kwamitin binciken kan alakarsa da shahrarren madamfari Ramon Abass aka Hushpuppi.

Ramon Abbas (Hushpuppi) wanda ake zargi da damfarar wani hamshakin attajiri, ya furta cewa ya ba Kyari cin hanci don kamo wani da ya nemi ya zarce shi a zambar dala miliyan 1.1.

Hukumar Bincike ta FBI, wata hukumar tabbatar da doka a Amurka ta zarge shi da hannu a wata harkallar damfara.

Ba tare da bata lokaci ba IGP na yan sanda ya dakatar da Abba Kyari kuma aka saukeshi da jagoranci rundunar IRT.

Kwamitin binciken da Sifeto Janar na yan sanda ya kafa karkashin jagorancin DIG Joseph Egbunike, ta zauna ne a hedkwatan FCID dake unguwar Area 10 Garki Abuja.

Kara karanta wannan

Karo na hudu, Abba Kyari ya gurfana gaban kwamitin bincike, an kwashe sa'a 4 yana shan tambayoyi

Asali: Legit.ng

Online view pixel