Karo na hudu, Abba Kyari ya gurfana gaban kwamitin bincike, an kwashe sa'a 4 yana shan tambayoyi

Karo na hudu, Abba Kyari ya gurfana gaban kwamitin bincike, an kwashe sa'a 4 yana shan tambayoyi

  • Abba Kyari ya sake gurfana gaba kwamiti a ranar Litinin
  • Wannan shine karo na hudu da zai gurfana don amsa tambayoyi kan zargin da ake masa
  • Hukumar FBI ta Amurka ta bukaci a mika mata Abba Kyari

Abuja - Tsohon kwamandan rundunar IRT, DCP Abba Kyari, ya sha tambayoyi na sa'o'i hudu yayinda ya sake gurfana gaban kwamitin binciken kan alakarsa da shahrarren madamfari Ramon Abass aka Hushpuppi.

Ramon Abbas (Hushpuppi) wanda ake zargi da damfarar wani hamshakin attajiri, ya furta cewa ya ba Kyari cin hanci don kamo wani da ya nemi ya zarce shi a zambar dala miliyan 1.1.

Hukumar Bincike ta FBI, wata hukumar tabbatar da doka a Amurka ta zarge shi da hannu a wata harkallar damfara.

Ba tare bata lokaci ba IGP na yan sanda ya dakatar da Abba Kyari kuma aka saukeshi da jagoranci rundunar IRT.

Kwamitin binciken da Sifeto Janar na yan sanda ya kafa karkashin jagorancin DIG Joseph Egbunike, ta zauna ne a hedkwatan FCID dake unguwar Area 10 Garki Abuja.

Kara karanta wannan

Amurka ta bukaci gaggauta garkame Abba Kyari cikin Kurkuku kafin ya gurfana a kotu

Majiyoyi sun bayyana cewa an tun karfe 2 na ranar Litinin da aka shiga yi masa tambayoyi, sai karfe shida na yamma aka tashi, Vanguard ta ruwaito.

Wannan shine karo na hudu da zai gurfana gaban kwamitin kuma yana cigaba da jaddada cewa shi babu laifin da yayi.

Karo na hudu, Abba Kyari ya gurfana gaban kwamitin bincike
Karo na hudu, Abba Kyari ya gurfana gaban kwamitin bincike, an kwashe sa'a 4 yana shan tambayoyi Hoto: Official PDP
Asali: Facebook

Akwai bukatar mika Abba Kyari ga FBI, ya fadi dalili

Shahararren lauyan nan mai fafutukar kare hakkin dan adam, Cif Femi Falana (SAN) ya yi kira ga Babban Lauyan Tarayya (AGF) kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, da ya aiwatar da bukatar Amurka ta mika mata Abba Kyari akan ka'ida.

A kalmomin sa yake cewa:

"Don kawo karshe da rufe wannan mummunan babi, binciken dole ne ya wuce tuhumar da FBI ta yi, dole ne a bincika lamarin a cikin gida, kuma ba wai a mika Kyari ga Amurka kawai ba.

Gaskiya za ta bayyana, kowa ya san bana karya: Abba Kyari ya sake jaddadawa

Kara karanta wannan

Hukumar Kwastam ta damke buhuhunan Shinkafa 314, buhuhunan dabino da Masara, a jihar Katsina

DCP Abba Kyari, ya jaddada cewa shi fa yana da gaskiya kan tuhumar da ake masa kuma nan ba da dadewa ba gaskiya zai bayyana.

Abba Kyari ya sake magana ne a jawabin da ya daura a shafin yanar gizon tsaffin wadanda suka halarci wani taro a Amurka.

Yace dukkan abubuwan da ya fada kuma ya daura a shafinsa gaskiya ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng