Shugaba Buhari ya taya Musulmai murnar shiga sabuwar shekara

Shugaba Buhari ya taya Musulmai murnar shiga sabuwar shekara

  • Buhari ya aika sakon gaisuwarsa ga Musulmai a Najeriya da fadin duniya
  • Sarkin Musulmai ya alanta ranar Talata a matsayin ranar farko ta watan Almuharram
  • Buhari ya ce Musulmai suyi koyi da koyarwan Manzon Allah

Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Talata, ya taya mabiya addinin Islama a Najeriya murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci 1443 bayan Hijran Manzon Allah (SAW).

Buhari ya aike sakonsa ne a jawabin da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya saki da yammacin Talata.

Shugaban kasan ya yi kira ga Musulmai suyi nazari kan muhimmancin Hijran manzon Allah da koyarwansa.

Buhari yace:

"Ina kira ga Musulmai su yi koyi da halayyar son juna, zaman lafiya da taimakekeniya. Ina taya dukkan Musulman shiga sabon shekara."

Shugaba Buhari ya taya Musulmai murnar shiga sabuwar shekara
Shugaba Buhari ya taya Musulmai murnar shiga sabuwar shekara Hoto: Presidency
Asali: Facebook

A Karon Farko, Babban Limamin Makka Sheikh Sudais Ya Naɗa Mata Mataimakansa

A bangare guda, kasar Saudiyya ta bayyana naɗa mata a manyan mukamai na hukumar dake kula da masallatai biyu mafiya daraja dake Makka da Madina.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Ba za'a tsige Uche Secondus daga jagorancin PDP ba, Tambuwal

A ranar Litinin ɗinnan ne kafar watsa labarai ta Al-Arabiyya tv, wadda mallakin Kasar Saudiyya ne, ta bada rahoto kan cigaban.

Shugaban hukumar, Sheikh Abdulrahman Al-Sudais ya naɗa mata guda biyu a matsayin mataimakansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng