Hukumar NYSC sai ta yi da gaske, an samu ‘Yan bautar kasa akalla 109 suna da COVID-19

Hukumar NYSC sai ta yi da gaske, an samu ‘Yan bautar kasa akalla 109 suna da COVID-19

  • Akwai ‘yan bautar kasa sama da 100 da aka samu dauke da COVID-19
  • Hukumar NYSC ta wajabta yin gwaji idan an shiga sansanin bada horo
  • Yaduwar Coronavirus ta fi kamari a jihohin Sokoto, Edo, Taraba, Filato

Najeriya - Hukumar NYSC ta shiga damu wa yayin da aka samu akalla matasa 109 da ke yi wa kasa hidima a halin yanzu da suke dauke da cutar COVID-19.

A karshen makon da ya gabata ne aka bude sansanin horas da ‘yan bautar kasa. A cikin sahun masu hidimar, an samu sama da matasa 100 dake da COVID-19.

Daily Trust ta ce hukumar NYSC ta gano hakan ne a sakamakon wajabta yin gwajin cutar da aka yi.

Alkaluman COVID-19 a jihohi

A jihar Edo, masu bautar kasa 17 aka samu da COVID-19 a lokacin da aka bude sansanin horaswar kamar yadda shugabar NYSC, Abiodun Olubukola, ta bayyana.

Haka zalika a sansanin NYSC da ke garin Mangun jihar Filato, an samu mutane 26 daga karshen makon jiya zuwa jiya, da aka tabbatar da Coronavirus ta harba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu ta hana gwamnatin Buhari kame Sunday Igboho

Shugabar NYSC ta jihar Gombe, Ada Imoni ta kafa wani kwamiti na musamman da zai yi yaki da COVID-19 bayan an gano matasa har 25 sun kamu da COVID-19.

Hukumar NYSC
'Yan bautar kasa Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

A Sokoto akwai ‘yan bautar kasa 14 da aka samu su na dauke da COVID-19. Kwamishinan lafiya na jihar Sokoto Dr. Ali Inname, ya shaida wa ‘yan jarida wannan.

Abin mamaki babu wani ‘dan bautar kasa da aka samu da cutar a Legas, amma an samu COVID-19 ta harbi matasa 21 a Taraba, da kuma mutane shida a jihar Ogun.

A Neja akwai mutane 18 daga cikin wadanda aka tura zuwa jihar domin su yi wa kasa hidima da aka samu da cutar inji kwamishinan labarai, Muhammed S. Idris.

Wadanda suka kamu da COVID-19 sun kara yawa

Alkaluman hukumar NCDC sun nuna ana samun karuwar masu dauke da wannan cuta. Mutane 851 aka samu da COVID-19 a kwanakin farko na Agustan nan.

Kara karanta wannan

Ayi hattara, sabon samufurin COVID-19 ya shiga Abuja, da wasu Jihohi 7 inji Gwamnatin Tarayya

Hakan na zuwa ne daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke cewa ayi hattara da samfurin Coronavirus wanda ya shigo Najeriya, kuma ya na kama mutane.

Rahotanni sun ce mutum 32 sun kamu da sabon samufurin COVID-19, don haka kwamitin PSC ya ware Jihar Akwa Ibom, ya ce annobar ta fi kamari a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel