Ayi hattara, sabon samfurin COVID-19 ya shiga Abuja, da wasu Jihohi 7 inji Gwamnatin Tarayya

Ayi hattara, sabon samfurin COVID-19 ya shiga Abuja, da wasu Jihohi 7 inji Gwamnatin Tarayya

  • Gwamnatin Tarayya ta ce har yanzu ba a ga karshen annobar COVID-19 ba
  • COVID-19 ta fi kamari a Abuja da irinsu Legas, Akwa Ibom, Filato, da Kano
  • Samufurin Delta ya shigo gari, mutane su na ta kamu wa a jihar Akwa Ibom

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ja-kunnen al’umma game da yaduwar samfurin Delta na kwayar cutar COVID-19, musamman a cikin wasu jihohi bakwai.

Jaridar Daily Trust ta rahoto sakataren gwamnatin tarayya, kuma shugaban kwamitin PSC, Boss Mustapha ya na wannan bayanin ranar Litinin a garin Abuja.

Mutanen Abuja da wasu jihohi shida su yi hankali

A cewar shugaban PSC, Boss Mustapha jihohin da aka fi samun cutar su ne: Legas, Akwa Ibom, Oyo, Ribas, Kano, Filato, Kwara, da babban birnin tarayya, Abuja.

Boss ya ce ana kokarin dakile yaduwar wannan nau’i na Coronavirus ganin yadda aka samu karin mutum miliyan hudu da suka kamu a Duniya a makon jiya.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotu Ta Dage Sauraron Karar Hadiman Sunday Igboho, Ta Fadi Dalili

“Idan aka kamanta adadin wadanda suke kamu wa da wadanda aka yi wa gaji, za a ga kai 6%, wannan abin tada hankali ne, har yanzu ba mu tsira ba.”

The Cable ta rahoto shugaban kwamitin shugaban kasar na PSC ya na cewa akwai bukatar a dage da yin gwaji, sannan ya ce an tsaurara matakan shige-da-fice.

COVID-19
COVID-19 ‘Delta Variant’ ya zo Najeriya Hoto: www.bbc.com/pidgin
Asali: UGC

Mutane 32 sun kamu da ‘Delta Variant’ – NCDC

An shiga juyi na uku na wannan annoba, yayin da gwamnatin tarayya ta ce mutane 32 aka tabbatar da sun kamu da sabon samfurin COVID-19 a kasar nan.

Shugaban NCDC, Dr. Chike Ihekweazu ya yi wannan jawabi a lokacin da ya yi bayanin halin da ake ciki. Daily Trust ce ta fitar da wannan rahoto a ranar Litinin

Dr. Chike Ihekweazu yake cewa 80% na mutanen da NCDC ta yi wa gwaji a jihar Akwa Ibom, suna dauke da samfurin wannan cutar wanda ya fi na bayan hadari.

Kara karanta wannan

An daure shugaban matasan PDP a gidan yari saboda ya zagi Buhari, SGF a Facebook

“Inda muka fi samun cutar shi ne Akwa Ibom. Daga cikin mutane 23 da ke da cutar, 19 suna dauke ne da samfurin kwayar Delta, shiyasa na ce 80% a Akwa Ibom.”

Akwai yiwuwar a sake dawo da takunkumi

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin tarayya na iya sake kafa dokar kulle a Najeriya saboda ɓarkewar cutar COVID19, wanda wannan shi ne karo na uku a kasar.

Amma ko za a sake sa dokar hana fita, kwamitin PSC yace ba dukan ƙasa abin zai shafa ba. Sabon samufurin cutar ya fi kamari ne a Abuja, Legas, da irinsu Akwa Ibom.

Asali: Legit.ng

Online view pixel