Da Ɗumi-Ɗumi: Hadiman Gwamna Su Uku Sun Juya Masa Baya, Sun Fice Daga PDP Sun Koma APC
- Hadiman gwamnan Taraba, Darius Ishaku, su uku sun fita daga PDP sun koma APC
- Ficewarsu na zuwa ne kwanaki uku bayan wasu yan PDP kimanin 50,000 sun koma APC a Taraba
- Ibrahim El-Sudi, shugaban APC na Taraba ya karbi sabbin mambobin yana mai cewa jam'iyyar na kara samun mambobi
Mashawarta na musamman ga Gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba su uku sun fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun koma All progressive Congress (APC), Daily Trust ta ruwaito.
Mashawartan gwamnan uku suna Audu Ade, Francis Fidelis da Kyauta Shehu Lau.

Asali: Facebook
Dukkansu ukun sun yi murabus daga mukamansu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A halin yanzu ba a bayyana dalilin da yasa hadiman gwamna suka fice daga PDP suka koma APC ba.
Ficewarsu daga jamiyyar yana zuwa ne kwanaki uku bayan fiye da magoya bayan jam'iyyar PDP '50,000' a yankin Kudancin Taraba sun koma APC.

Kara karanta wannan
2023: Gagarumin nasara yayin da sama da mutum 50,000 suka bar PDP da APGA zuwa APC a jihar Taraba
Shugaban APC na jihar Taraba ya karbi tsaffin hadiman gwamnan
Shugaban jam'iyyar APC a jihar, Barrister Ibrahim El-Sudi, wanda ya karbi mashawartan na musamman uku, ya ce jam'iyyarsu na kara samun magoya baya a kullum.
Ya kuma bayyana cewa jam'iyyar ta kammala dukkan shirye-shirye domin yin tarurukan da zaben shugabannin mazabu.
A jawabin da ya yi wurin taron manema labarai, shugaban kwamitin shirya tarurukan APC a jihar Taraba, Alhaji Saidu Usman Dakingari, tsohon gwamnan jihar Kebbi, ya ce mambobin kwamitin sun tafi jihar ne domin yin taron.
Sai dai, ya kuma nemi goyon bayan da hadin kai daga 'ya'yan jam'iyyar domin ganin an yi zaben da tarurukan cikin lafiya.
Sauya Sheƙa: Wasu Ƴan APC Sun Cinnawa Tsintsiyarsu Wuta, Sun Ce Suna Neman Mafaka a Ƙarƙashin Lemar PDP
A wani labarin daban, mun kawo muku cewa kimanin yan jam'iyyar All Progressives Congress, APC, su 100 ne suka koma jam'iyyar Peoples Democratic Party a ranar Laraba a karamar hukumar Oshimili South ta jihar Delta, The Punch ta ruwaito.
Masu sauya shekan, wadanda suka cinnawa tsintsiyarsu wuta, sun ce suna neman mafaka ne a karkashin inuwar leman jam'iyyar PDP.
Okonji, wanda ya karbi wadanda suka sauya shekan a sakatariyar jam'iyyar PDP a Asaba, ya bukaci mambobin PDP su yi amfani da damar cigaba da rajistan masu zabe da INEC ke yi ta intanet su samu katin zabensu.
Asali: Legit.ng