Sauya Sheƙa: Wasu Ƴan APC Sun Cinnawa Tsintsiyarsu Wuta, Sun Ce Suna Neman Mafaka a Ƙarƙashin Lemar PDP

Sauya Sheƙa: Wasu Ƴan APC Sun Cinnawa Tsintsiyarsu Wuta, Sun Ce Suna Neman Mafaka a Ƙarƙashin Lemar PDP

  • Wasu mambobin jam'iyyar APC a karamar hukumar Oshimili ta Kudu a jihar Delta sun koma PDP
  • Masu sauya shekar su 96 sun cinnawa tsintsiyarsu wuta sun ce suna son mafaka a lemar PDP
  • Dada Okonji, shugaban PDP na Oshimili ne ya karbi masu sauya shekar a sakatariyar PDP a Asaba

Asaba, Jihar Delta - Gabanin babban zaben 2023, kimanin yan jam'iyyar All Progressives Congress, APC, su 100 ne suka koma jam'iyyar Peoples Democratic Party a ranar Laraba a karamar hukumar Oshimili South ta jihar Delta, The Punch ta ruwaito.

Masu sauya shekan, wadanda suka cinnawa tsintsiyarsu wuta, sun ce suna neman mafaka ne a karkashin inuwar leman jam'iyyar PDP.

Sauya Sheƙa: Wasu Ƴan APC Sun Cinnawa Tsintsiyarsu Wuta, Sun Ce Suna Neman Mafaka a Ƙarƙashin Lemar PDP
Tambarin Jam'iyyar APC da PDP. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

The Punch ta ruwaito cewa sun yi jawabi ne yayin taron masu ruwa da tsaki da shugaban PDP na karamar hukumar Oshimili ta Kudu, Dada Okonji ya kira.

Okonji, wanda ya karbi wadanda suka sauya shekan a sakatariyar jam'iyyar PDP a Asaba, ya bukaci mambobin PDP su yi amfani da damar cigaba da rajistan masu zabe da INEC ke yi ta intanet su samu katin zabensu.

Kara karanta wannan

'Wannan na shan ruwa ne': Ƴan bindiga da suka sace mai AZECO Pharmacy sun ƙi karɓar N10m, sun ce N30m suke so

Ya ce:

"Mun yi farin cikin karbar yan APC 96 a yau. Muna gode wa Gwamna Okowa bisa ayyukan da ya yi a Oshimili South. Ba za mu iya dena masa godiya ba bisa ayyukan da ya yi ba na gine-gine da cigaban mutane ds.
"Don haka, yana da muhimmanci mambobinmu su samu katinsu na zabe gabanin zabe mai zuwa. Wadanda ba su da shi; wadanda yanzu sun cika shekaru 18 da wadanda suka canja gari suka dawo karamar hukumar su tafi su yi rajista da INEC."

Ya zaburar da masu rike da mukaman siyasa a karamar hukumar su kara kaimi wurin tallafawa mutane da jam'iyyar ke yi da aka dakatar saboda zabe, ya kuma bada tabbacin PDP za ta lashe dukkan zabukan don cancantarta.

2023: Ku Tashi Ku 'Ƙwace' Mulki Daga Hannun Dattijai, Gwamna Ya Zaburar Da Matasan Nigeria

A wani labari daban, Yahaya Bello, Gwamnan Jihar Kogi ya ce matasan Nigeria ba su nuna wa dattijai cewa 'lallai da gaske suke son karɓe shugabancin kasa ba', rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Manyan shugabannin PDP sun sauya sheka zuwa APC, an saki sunayensu

Bello, wanda tuni ya bayyana niyyarsa na yin takarar shugabancin kasa, a ranar Talata ya yi kira ga matasa su yi aiki don ganin sun 'ƙarbe' mulki daga hannun dattawa gabanin zaben 2023.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a ranar Talata a Ijebu-Ode, jihar Ogun, a wurin wani taro da aka yi wa laƙabin: "Matasa ke da iko a hannun su'.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel