Barewa ba ta gudu: Yaron Ministan shari’a, Malami, ya yi gado, ya zama sabon Lauya
- A jiya ne Abdulazeez Abubakar Malami ya zama sabon Lauya a Najeriya
- Yaron Ministan shari’ar ya na cikin jerin Lauyoyin da aka yaye a Abuja
- Abdulazeez Malami ya dauki hoto tare da iyalinsa bayan bikin rantsarwa
Daya daga cikin ‘ya ‘yan Ministan shari’a na kasa, Abdulazeez Abubakar Malami, ya na cikin lauyoyin da aka yaye a farkon makon nan a Najeriya.
A ranar Talata, 27 ga watan Yuli, 2021, aka yaye lauyoyi 880, aka ba su damar yin aikin lauya bayan sun kammala makarantar koyon ilmin shari’a.
Abdulazeez Abubakar Malami ya zama Lauya
Daily Trust ta ce Abdulazeez Abubakar Malami ya na cikin sanannun lauyoyin da aka yaye a ranar Talata.
Bayan an kammala bikin yaye sababbin lauyoyin a birnin tarayya Abuja, Abdulazeez Abubakar Malami ya dauki hotuna dauke da kayansa na lauyoyi.
This Nigeria ta kawo hotunan matashin lauyan a cikin alkyabba da hular lauyoyi, tare da mai dakinsa, Khadija Abduljalil Danbatta da diyarsu a hannu.
Kyawun 'da ya gaji ubansa
Babu shakka Abdulazeez Abubakar Malami ya bi sahun mahaifinsa, Abubakar Malami, wanda shi ne Ministan shari’a, kuma babban lauyan gwamnati.

Asali: UGC
Bayan haka AGF, Abubakar Malami ya kai matsayin babban lauya a Najeriya watau SAN. A shekarar 1992 ya fara aiki, kamar yadda ‘dansa ya zama.
Ministan shari’an ya karanta ilmin shari’a da gudanarwa a jami’o’in tarayya na Usman Danfodio da ke Sokoto, da ta UNIMAID shekaru 30 da suka wuce.
A watan Yulin shekarar bara ne Abdulazeez Malami ya angwance da sahibarsa, Khadija Danbatta a Kano, bayan shekara daya sai ga shi ya zama Lauya.
A daidai wannan lokaci kuma ake jin cewa kungiyar ASUU ta cigaba da rigima da gwamnatin Muhammadu Buhari a kan manhajar biyan albashi na IPPIS.
Ma’aikatar ilmi da Malaman Jami’o’in Gwamnati suna musayar kalamai a Najeriya. Hakan ya nuna akwai yiwuwar a sake shiga wani yajin-aiki a kasar.

Asali: UGC
Asali: Legit.ng