Sabon yajin-aiki ya na jiran dubunnan daliban Jami’o’i a dalilin sabanin ASUU da Gwamnati

Sabon yajin-aiki ya na jiran dubunnan daliban Jami’o’i a dalilin sabanin ASUU da Gwamnati

  • Gwamnatin Tarayya ta maida wa ASUU martani game da zargin saba alkawari
  • Kungiyar ASUU ta ce gwamnati ta yi watsi da yarjejeniyar da ta sa hannu a 2020
  • Ma’aikatar ilmi ta yi karin-haske, ta fadi dalilin cigaba da biyan ASUU ta IPPIS

Abuja - A ranar Talata, 27 ga watan Yuli, 2021, gwamnatin tarayya ta musanya zargin cewa ta saba yarjejeniyar da ta yi da kungiyar malaman jami’a.

Abin da Malaman jami’a suke fada ba gaskiya ba ne - FG

Jaridar Punch ta rahoto gwamnatin tarayya ta na cewa zargin da kungiyar ASUU ta ke yi na cewa ba ta cika alkawuran da ta dauka ba, ba gaskiya ba ne.

Mai magana da yawun ma’aikatar ilmi na kasa, Ben Gong, ya yi hira da Punch a Abuja, inda ya bayyana abin da ya sa gwamnati ba ta karbi UTAS ba.

Ben Gong yake cewa manhajar UTAS da kungiyar ASUU ta kawo domin a rika biyan malaman jami’a albashi da shi, bai yi tanadi na karbar haraji ba.

Kara karanta wannan

Dattijon Arewa ya caccaki mulkin APC, ya ce za ta ruguza Najeriya kafin 2023

Gong ya ce ba zai yiwu malaman jami’a su rika karbar albashi ba tare da an cire masu haraji ba.

“Kungiyar ASUU ta fito da zargin da ta ke yi. Su fadi wace yarjejeniya mu ka saba. Su fadi ma’aikatun da suka saba alkawarin da aka yi.”

FUTO, Akure
Jami'ar fasaha ta tarayya da ke Akure Hoto: allafrica.com
Asali: UGC

ASUU: Akwai yadda za a rika cire mana haraji a manhajar UTAS

Kungiyar ASUU ta karyata Gong, ta ce ya na magana ba tare da ya tuntubi iyayen gidansa ba.

“Ya na nan a lokacin da aka jarraba manhajar UTAS da zai ce babu damar karbar haraji? Kowace ma’aikata ta na nan aka duba manhajar, majalisa ta yaba da ita.”

ASUU ta ce baya ga batun daina amfani da IPPIS, gwamnatin tarayya ba ta saki kudin gyara jami’o’i ba, sannan ba a fara sa alawus a cikin albashinsu ba.

“An yarda cewa za a gyara dokar hukumar kula da jami’o’i, NUC, ta yadda ba za a cika ko ina da jami’o’i ba, dole sai an kai maganar zuwa majalisar tarayya.”

Kara karanta wannan

Hatta Musa Ya Yi Hijira Saboda Fir'auna, Babu Laifi Don Igboho Ya Tsere, Afenifere

Kungiyar ASUU ta na iya koma wa yajin-aiki

Kun ji labari malaman Jami’a sun fara barazanar sake yin jajin-aiki a Najeriya. ASUU ta ce har gobe gwamnatin tarayya ba ta cika alkawarin da aka yi da ita ba.

IPPIS na cikin sabanin gwamnatin tarayya da malaman kamar yadda shugaban kungiyar ASUU na jami’ar, Abubakar Tafawa Balewa, Dr. Ibrahim Inuwa ya fada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel