Wani sabon yamutsi ya na jiran Shugabannin APC a kan yadda za ayi rabon kujeru na kasa

Wani sabon yamutsi ya na jiran Shugabannin APC a kan yadda za ayi rabon kujeru na kasa

Jam’iyyar APC ta na tunanin fito da shugabanni ba ta hanyar shirya zabe ba

Wasu masu neman zama Shugaban Jam’iyya ba su yarda da wannan batu ba

‘Yan takarar sun hakikance a kan dole ayi zabe, ba a kakaba shugabanni ba

Kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC na gwamna Mai Mala Bunin a iya samun sabuwar matsala a a kan shirin da aka dauko na fitar da shugabanni.

Jaridar This Day ta kawo rahoton cewa maganar zaben ‘yan takara ba tare da an gudanar da zabe ba, zai iya kawo matsala tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyar ta APC.

Magoya-bayan tsofaffin gwamnonin Nasarawa, Umaru Tanko Al-Makura da Abdullahi Adamu ba su goyon bayan sabon salon da ake ta kokarin shigo wa da shi.

Haka zalika yaran tsohon gwamnan jihar Benuwai, Sanata George Akume sun karfafi ra’ayoyin Sanata Umaru Al-Makura da Sanata Adamu na shirya zabuka.

Dalilin kawo tsarin yi wa 'yan takara i'itifaki

Kara karanta wannan

2023: Jigon APC ya ambaci wanda ake zargin APC za ta ba takarar Shugaban kasa

Sakataren rikon kwarya na APC, Sanata John Akpanudoedehe ya ce ana tunanin yi wa ‘yan takara i’itifaki ne saboda gwamnonin PDP da suka shigo jam’iyyar.

John Akpanudoedehe ya na ganin hakan zai takaita rikicin da za iya samu wajen zaben shugabanni.

Shugaban APC
Mai Mala Buni Hoto: @Maistrategy
Asali: Facebook

Hakan ba za ta sabu ba a jam'iyyar APC - Adamu, da sauransu

Magoya bayan Al-Makura, Adamu, da Akume, wadanda duk suna harin kujerar shugaban jam’iyyar APC na kasa, ba su goyon-bayan wannan ra’ayin.

Wani daga cikin masu yi wa Sanata Umaru Al-Makura yakin neman zabe, ya bayyana cewa ba za su goyi-bayan wani tsari da ba zabe ba, domin siyasa ake yi.

“Damakaradiyya ce, mu je mu shiga zaben, ‘dan takarar da ya fi farin jini ya yi nasara. A kowane zabe akwai masu yin galaba, akwai marasa samun nasara.”

Shugaban yakin neman zaben Abdullahi Adamu, ya ce idan aka bi ta John Akpanudoedehe, za a kakaba wa jam’iyyar APC wasu ‘yan takara ne marasa farin jini.

Kara karanta wannan

"Ka kiyaye ni," Gwamnan Zamfara ya gargadi mataimakinsa

Haka zalika wani na-kusa da Ministan harkoki na musamman, Akume, ya shaida wa jaridar cewa duk wani tsari da aka shigo da shi zai iya kawo rikici a APC.

Idan mu ka koma siyasar Kano, za a ji cewa an nada kwamitin mutum bakwai da zai binciki Yunusa Dangwani da Yusuf Danbatta a kan zargin neman takara.

Ana zargin ‘Yan Kwankwasiyyar da laifin neman cin amanar jam’iyyar PDP, sannan ba su tare da ‘Dan takarar Mai gidansu, Sanata Rabiu Kwankwaso, Abba Gida-Gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel