Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi Ingila yau ganin Likita, da halartan taro

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi Ingila yau ganin Likita, da halartan taro

  • Kuma dai, Buhari zai sake shillawa kasar Sarauniya Lillybet
  • Fadar shugaban kasa tace zi tafi halartan taron kasa da kasa kan inganta Ilimi
  • Daga baya ya dan huta a Ingila da ganin Likitocinsa

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Litinin, 26 ga Yuli, zai shilla kasar Birtaniya ganin Likitocinsa da kuma halartan taron ilimi na duniya kan hadin kai wajen zuba kudi fagen ilimi watau GPE 2021-2025.

Mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ta shafinsa na Facebook.

Ya bayyana cewa bayan taron, Buhari zai ga Likitocinsa domin duba lafiyarsa sannan ya dawo Najeriya bayan makonni biyu tsakiyar Agusta.

Adesina yace:

"Taron wanda Firai Ministan Birtaniya, Boris Jonhson da shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta suka shirya, zai hada kan shugabannin kasashe wajen fitar da manhajar hadin kai wajen kawo sauyi lamarin ilimi."
Bayan haka shugaba Buhari zai yi zaman diflomasiyya da Firai Minista Boris Johnson."

Kara karanta wannan

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira Landan, inda zai kwashe makonni biyu

"Bayan taron, shugaban kasa zai kwashe yan kwanaki domin ganin Likitansa da ya kamata ace ya gani tun a baya. Zai dawo Najeriya a tsakiyar Agusta, 2021."
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi Ingila yau ganin Likita, da halartan taro
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi Ingila yau ganin Likita, da halartan taro Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Adesina ya kasa cewa Buhari zai samu rakiyar Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; karamin ministan Ilimi, Emeka Nwajuiba; NSA Babagana Munguno, da shugaba NIA, Ahmed Rufai Abubakar.

Wata daya kenan da dage tafiyarsa zuwa Landan

Za ku tuna cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dage tafiyarsa zuwa Landan don ganin likita har sai baba-ta-gani.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel