Yanzun nan: Sunday Igboho ya saduda, ya fasa yin gangamin Yarbawa a Legas bayan an sace matarsa

Yanzun nan: Sunday Igboho ya saduda, ya fasa yin gangamin Yarbawa a Legas bayan an sace matarsa

  • Sunday Igboho ya bayyana dakatar da gangamin da aka shirya gudanawar wa a Lagos ranar Asabar
  • Ya bayyana haka a wata hira da yayi da BBC Pidgin biyo bayan kai harin yan bindiga gidan sa na Ibadan tare da garkuwa da matar sa
  • Kalaman nasa na zuwa bayan kungiyar hadin kan Yarabawa ta bayyana ba gudu ba ja da baya a gudanar da gangamin kamar yadda aka tsara

Dan gwagwamayar Yarabawa, Sunday Adeyemo Igboho, ya dakatar da gangamin kasar Yoruba da aka shirya gabatarwa a Lagos ranar Asabar, The Cable ta ruwaito.

Idan za a iya tunawa masu fafutukar kafa kasar Yoruba sun gudanar da gangami a sassan kudu maso yamma tare da shirya gudanar da na Lagos ranar Asabar.

Sunday Igboho
Sunday Igboho dan gwagwarmayar kafa kasar Yarbawa. Hoto: The Cable
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Dan Majalisar PDP ya bayyana halin da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle zai tsinci kansa a 2023

Sai dai, Igboho a tattaunawar da yayi da BBC Pidgin, ya bayyana cewa an dakatar da gangamin na Lagos.

Ya bayyana haka yan awanni bayan kai hari gidan sa na Ibadan, Jihar Oyo wanda aka ruwaito yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da garkuwa da matar sa.

Kalaman sa na zuwa ne bayan sanarwar da kungiyar hadin kan Yarabawa, Ilana Omo Oodua, ta fitar cewa za a gudanar da gangamin na Lagos ranar Asabar kamar yadda aka tsara.

Sanarwar na dauke da sa hannun shugaban ta, Emeritus Professor Banji Akintoye, tare da raba samfurin ta ga manema labarai ta hannun mai magana da yawun sa, Mr. Maxwell Adeleye.

KU KARANTA: FG ta bayyana gwamnonin Nigeria biyu da Nnamdi Kanu ya so ya kashe su

"Muna so mu sake tabbatar da cewa gangamin kafa kasar Yarabawa da aka tsara ranar Asabar, 3 ga watan Yuli, a Jihar Lagos zai gudana kamar yadda aka tsara" a wani sashen sanarwar.

Ku saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel