'Dan Majalisar PDP ya bayyana halin da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle zai tsinci kansa a 2023

'Dan Majalisar PDP ya bayyana halin da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle zai tsinci kansa a 2023

  • Dan majalisar tarayya daga Jihar Kogi Yusuf Tajuddeen ya soki Gwamna Matawalle bayan komawar sa APC
  • Yusuf, dan jam'iyyar PDP ya ce gwamnan bashi da nagarta da wata jam'iyya za ta yi alfahari da shi
  • Dan majalisar ya kara da cewa gwamnan zai zama abin tausayi tamkar marayar dan siyasa saboda bashi da zai samu damar yin tazarcen a 2023 ba

Tajjudeen Yusuf, dan majalisar wakilai na tarayya daga jihar Kogi, ya ce Bello Matawalle gwamnan Zamfara dan siyasa ne da ke neman tazarce ido rufe, The Cable ta ruwaito.

Yusuf, dan majalisar tarayya na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya bayyana hakan ne yayin martani game da sauya shekar Matawalle zuwa jam'iyyar APC a ranar Talata.

Gwamnonin jam'iyyar APC yayin tarbar Gwamna Bello Matawalle
Gwamnonin jam'iyyar APC yayin tarbar Gwamna Bello Matawalle a Zamfara. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Mafarauta sun ɗirka wa mai garkuwa harsashi ya mutu yayin da yazo karɓar kuɗin fansa

A wata sanarwa ranar Laraba, dan majalisar na Kogi ya zargi Matawalle da rashin aiki, ya kara da cewa gwamnan Zamfaran dan siyasa ne da ba jam'iyyar da za ta yi alfahari da shi kamar yadda The Cable ta ruwaito.

"Kowa dole ya nemi yadda zai yi; abin bakin ciki ne tun da Matawalle ya zama gwamna, ya ke ta neman yadda za a yi ya zarce saboda ba yadda za a yi da irin rashin kokarin sa da kuma karuwar matsalar tsaro a karkashin sa," in ji dan majalisar.
"A zahirin gaskiya, ba irin dan siyasar da wata jam'iyya za ta yi alfahari da shi bane, ta kowacce irin hanya; cigaban kasa, cigaban dan adam, samar da tsaro ga al'umma da sauran wuri da dama, ya gaza a fannoni da dama.

KU KARANTA: Nnamdi Kanu na samun goyon bayan dillalan makamai na ƙasashen waje, Dattawan Arewa

"Jami'iyya mara kan gado ce kadai za ta nuna murna ga mutumin da ba shi da mamora, ba shi da mamora a siyasance da sauran fannoni; su je da shi mu kuma muna shirin kawo wanda ya fi shi a zabe na gaba.
"Bayan duka tulin alkawuran 2014, APC ta nuna gazawa a duka bangarori, a haka, zaka ga wasu gwamnoni da jigajigan gwamnatin tarayya suna barin ayyukan su don tarbar wanda ya gaza."
Dan majalisar ya kara da cewa Matawalle "ya ciza hannun da ya shayar da shi" kuma "ya siyawa kansa zama abin tausayi a siyasa a kakar zabe ta 2023".

Masu Riƙe Da Muƙaman Siyasa a Kebbi Sun Sadaukar Da Rabin Albashinsu Don Yaƙar Ƴan Bindiga

A wani labarin daban, masu rike da mukaman siyasa a jihar Kebbi sun sadaukar da rabin albashinsu na watan Yuni ga gwamnatin jihar domin bada gudunmawa wurin yaki da 'yan bindiga a jihar, News Wire ta ruwaito.

Sakataren gwamnatin jihar, Babale Yauri ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Birnin Kebbi.

Sakataren gwamnatin ya jadada muhimmancin da ke da akwai wurin ganin an samu hadin kai da zaman lafiya a jihar domin shine zai haifar da cigaba a jihar da kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel