FG ta bayyana gwamnonin Nigeria biyu da Nnamdi Kanu ya so ya kashe su

FG ta bayyana gwamnonin Nigeria biyu da Nnamdi Kanu ya so ya kashe su

  • Gwamnatin Nigeria ta ce Nnamdi Kanu zai amsa tambayoyi game da hare-haren da ake kai wa a yankin kudancin Nigeria
  • Ma'aikatar harkokin kasar waje ta sanar da jakadodin kasashen Yamma wasu zargi da ake yi wa shugaban na IPOB
  • Gwamnatin tarayya ta soki Kanu saboda kafa kungiyar masu tada kayan baya da aka fi sani da Eastern Security Network, ESN

Gwamnatin tarayya ta zargi shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, da yin barazanar kashe wasu gwamnoni biyu a yankin kudu maso gabas.

Gwamnatin ta Nigeria ta yi wannan zargin ne a cikin wasikar da ta aike wa jakadodin kasashen Yamma kamar yadda kamfanin dillanci labarai ta NAN ta ruwaito.

Willie Obiano
Gwamna jihar Anambra Willie Obiano. Hoto: Chief Willie Obiano
Asali: Facebook

Kanu ya ce Obiano gawa ne da ke tafiya

Ma'aikatar harkokin kasar wajen cikin wasikar mai kwanan wata na 26 ga watan Afrilun 2021, ta ce daya daga cikin gwamnonin da shugaban na IPOB ya yi barazanar kashewa shine Gwamna Willie Obiano na jihar Anambra.

A cewar gwamnatin, Kanu ya bayyana Obiano a matsayin gawa da ke tafiya.

Wasikar ta yi nuni da wasu barazanar da Kanu ya yi kamar haka:

"Wannan shine abin da muke son yi. Obiano (Gwamnan jihar Anambra) daga yau, duk inda muka hadu da kai a waje za mu kai maka hari ... Obiano ... kai gawa ne da ke tafiya."

Gwamnatin ta Nigeria ta kuma ce wani gwamna daga yankin da aka yi wa barazana shine Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia, shima an tabbatar Kanu ya fadawa mabiyansa su kashe shi kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Wasikar ta kuma ce yan IPOB sun kai hari gidan gwamna Hope Uzodinma a kauyensu sun masa barna.

Nnamdi Kanu na samun goyon bayan dillalan makamai na ƙasashen waje, Dattawan Arewa

A wani labarin, kungiyar tuntuba ta Arewa, ACF, ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi takatsantsan da lamarin shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, rahoton Daily Sun.

A cewar kungiyar ta Arewa, shugaban na masu fafutikan kafa kasar Biafra yana da abokan hulda sosai a kasashen ketare.

Kungiyar ta yi wannan furucin ne yayin da ta ke martani kan sake kama shugaban na IPOB a ranar Talata 29 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel