Da dumi: Yan bindiga sun fasa Otal a Abuja, sun kwashe mutane

Da dumi: Yan bindiga sun fasa Otal a Abuja, sun kwashe mutane

  • Matsalar tsaro na cigaba da kamari a birnin tarayya Abuja
  • Wannan shine karo na biyar da aka kai hari garin Tunga Maje
  • Tunja Maje na kusa da iyakar birnin tarayya da jihar Neja

Wasu yan bindiga sun kai farmaki gidan Otal na Hilltop dake garin Tunga Maje a birnin tarayya Abuja da daren Laraba, 24 ga Yuni, 2021.

Daily Trust ta rahoto cewa sun yi awon gaba da mamallakin Otal din tare da wasu mutane.

An ce mamallakin Otal din mai sune Prince Adejo, tare da wasu mutane shida na ganawa a ciki lokacin da yan bindigan suka kai farmaki.

Garin Tunan-Maje ta kwan biyu tana fuskantar barazanar yan bindiga.

A cewar mazauna garin, wannan shine karo na biyar da aka kai hari don garkuwa da mutane a shekarar nan.

KU KARANTA: Yan sanda sun arce yayin da sojoji suka kutsa caji ofis a Osun

Da dumi: Yan bindiga sun fasa Otal a Abuja, sun kwashe mutane
Da dumi: Yan bindiga sun fasa Otal a Abuja, sun kwashe mutane
Asali: UGC

DUBA NAN: An rufe yin rijistan Hajjin Bana a Saudiyya, mutum 540,000 suka yi rijista, za'a zabi 60,000

Wani mazaunin garin ya bayyanawa Daily Trust cewa yan bindiga kimanin mutum 10 sun fasa cikin Otal din ne misalin karfe 10:30 na dare.

Ya ce sai da sukayi harbe-harben bindiga don tsoratar da mutane kafin garkuwa da wadanda suka zo nema.

Daga cikin wadanda aka sace, an ce akwai tsohon dan majalisar jihar Kogi, Friday Sani Makama.

Har yanzu masu garkuwa da mutanen basu tuntubi iyalan wadanda suka sace ba.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, ASP Mariam Yusuf, ta tabbatar da aukuwan lamarin.

Tace: "Hukumar ta kaddamar shirin ceto wadanda aka sace ba tare da sun samu wan rauni ba."

An sace dimbin mutane a jihar Kaduna

A bangare guda, akalla mutum daya ya rasa rayuwarsa yayinda akayi awon gaba da mutum 33 yayinda yan bindiga suka kai hari karamar hukumar Kachia dake jihar Kaduna.

Yan bindigan sun kai wannan hari ne a dare cikin garin Kachia kuma sun jikkata mutane da dama, rahoton ChannelsTV.

Hakimin garin Kachia, Idris Suleiman ta tabbatar da aukuwan wannan lamari yayinda jami'an tsaro da kwamishanan tsaron jihar, Samuel Aruwan, suka kai ziyara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel