Kuma dai: Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 33 a Kaduna, sun hallaka mutum 1

Kuma dai: Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 33 a Kaduna, sun hallaka mutum 1

  • Jihar Kaduna na cigaba da fuskantar barazanar tsagerun yan bindiga
  • Gwamnatin jihar ta tsaya kan bakanta cewa ba zatayi sulhu da yan bindigan ba
  • Bayan an samu sauki tare hanyar Kaduna/Abuja, yanzu sun koma bi gida-gida

Akalla mutum daya ya rasa rayuwarsa yayinda akayi awon gaba da mutum 33 yayinda yan bindiga suka kai hari karamar hukumar Kachia dake jihar Kaduna.

Yan bindigan sun kai wannan hari ne a dare cikin garin Kachia kuma sun jikkata mutane da dama, rahoton ChannelsTV.

Hakimin garin Kachia, Idris Suleiman ta tabbatar da aukuwan wannan lamari yayinda jami'an tsaro da kwamishanan tsaron jihar, Samuel Aruwan, suka kai ziyara.

Yadda harin ya auku

Suleiman ya ce yan bindigan sun dira cikin garin misalin karfe 9 na daren Alhamis kuma suka fara harbin kan mai uwa da wabi.

Ya ce da farko sun kai farmaki gidan Burosi inda sukayi sace mutum biyar kuma suka kashe direban mai gidan Burodin.

Daga bisani suka shiga unguwar MotherCat kuma suka sace mutum 28, cikin har da mai juna biyi.

Ya kara da cewa kafin suka fita daga cikin garin, sai da suka kwashe kayayyakin yan kasuwa.

Jihar Kaduna na cigaba da fuskantar kalubalen rashin tsaro.

KU KARANTA: Dalilin da Buhari da APC suka gaza a cikin shekara hudun farko — Shugaban Majalisar Dattijai Ahmed Lawan

Kuma dai: Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 33 a Kaduna, sun hallaka mutum 1
Kuma dai: Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 33 a Kaduna, sun hallaka mutum 1

DUBA NAN: Najeriya ta talauce, wajibi ne mu cigaba da karban bashi: Shugaban Majalisa

Karo na farko, an sace dalibai a Kebbi, El-Rufa'i na Kaduna yayi tsokaci

Nasir el-Rufai, gwamnan Kaduna, ya ce sace yara ‘yan makaranta da aka yi kwanan nan a Kebbi ba alama mai kyau ba ne ga lamarin tsaro a arewa maso yamma.

El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kaiwa Atiku Bagudu, gwamnan Kebbi, a ranar Alhamis.

A ranar 17 ga watan Yuni, wasu ‘yan bindiga sun kai hari Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri, Kebbi, suka yi awon gaba da dalibai da malamai da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel