Dalibin aji karshe ya shigar da jami'a kotu bayan an koreshi don ya zagi gwamna a Facebook

Dalibin aji karshe ya shigar da jami'a kotu bayan an koreshi don ya zagi gwamna a Facebook

  • Wani dalibi ya shigar da jami'ar jihar Akwa Ibom Kotu kan korarsa da akayi don ya zagi gwamna a Soshiyal Midiya
  • Dalibin mai suna Iniobong Ekpo, wanda dan aji karshe ne ya bukaci jami'ar ta biyashi N20m
  • Bayan dakatad da shi, an hana shi shiga jami'ar

Wani dalibin Najeriya mai suna Iniobong Ekpo, ya shigar da jami'ar jihar Akwa Ibom kotu kan korarsa da tayi kan abin da ya daura a kafar ra'ayi da sada zumunta na suka gwamnan jihar, Udom Emmanuel.

A cewar Soaznews Etv, jami'ar ta bayyana korar dalibin a wasikar da ta aike ranar 9 ga Afrilu, 2021 saboda rashin da'ar da ya yi. Hakazalika tace wannan ya sabawa dokar jami'ar.

Rijistarn jami'ar Joh E Udo, wanda ya rattafa hannu kan wasikar ya kara da cewa an haramtawa dalibin shiga jami'ar.

Yanzu haka ya shigar da jami'ar kotu kuma ya bukaci a biyashi kudi N20m, kuma a rabu da shi ya cigaba da karatunsa.

KU KARANTA: Dalilin da Buhari da APC suka gaza a cikin shekara hudun farko — Shugaban Majalisar Dattijai Ahmed Lawan

Dalibin aji karshe ya kai makarantarsa kotu
Dalibin aji karshe ya shigar da jami'a kotu bayan an koreshi don ya zagi gwamna a Facebook Hoto: Soaz ETv
Asali: Facebook

DUBA NAN: Najeriya ta talauce, wajibi ne mu cigaba da karban bashi: Shugaban Majalisa

Abinda dalibin da daura a Facebook

Premium Times ta ruwaito cewa dalibin wanda ke karatu a tsangayar injiniyancin aikin noma ya tuhumci gwamnan da laifin rashin cika alkawarin da yayi daliban da aka yaye a 2017.

Yace:

"Shekaru biyu da kwanaki 166 bayan alkawarin da yayi, har yanzu babu ko mutum guda cikin daliban da aka yaye da ya samu ko Naira guda duk da cewa wadanda suka fita da 1st Class sun je ofishinsa amma basu gansa ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel