Abu 6 da ya kamata ka sani kan Farouk Lawan, mutumin da aka jefa Kurkuku

Abu 6 da ya kamata ka sani kan Farouk Lawan, mutumin da aka jefa Kurkuku

  • Farouk Lawan ya shafe shekara takwas yana kai gwauro da mari a zaurukan kotuna daban daban
  • Binciken badakalar tallafin mai ne a 2012 da kwamitin da ya shugabanta ya janyo masa aikata rashawar
  • Ya yi shuhura a zauren majalisar na tsawon shekara 16

Farouk Lawan, tsohon dan majalisar wakilai wanda aka yanke wa hukunci daurin shekara bakwai a gidan yari ranar Talata, sanannen suna ne a zauren majalisar wakilan tarayya.

Bayan share shekara takwas ana tafka shari’a , daga karshe dai wata kotun babban birnin tarayya ta yanke hukunci a kan shari’ar da ta shafi cin hanci da rashawa da ake yi wa dan majalisar, wanda ake yi wa lakabi da ‘Mai Nagarta/Gaskiya.’

An daure shi ne bayan da aka same shi da laifin karbar rashawa daga attajirin dan kasuwan nan Femi Otedola, a lokacin binciken tallafin mai a 2012.

Femi Otedola ya zargi Lawan din da neman a ba shi Dala miliyan uku domin wanke kamfanin mai da iskar gas na Zenon Petroleum and Gas Limited, daga jerin kamfanonin da ake bincikar su a lokacin.

KU KARANTA: Dan Achaba ya gudu daga asibiti bayan samun labarin matarsa ta haifi ’yan biyu

Abu 6 da ya kamata ka sani kan Farouk Lawan, mutumin da aka jefa Kurkuku
Abu 6 da ya kamata ka sani kan Farouk Lawan, mutumin da aka jefa Kurkuku
Asali: Facebook

KU KARANTA: Waiwayen Tarihi: Gagarumar gobarar da ta faru a Mina a Hajjin 1997

Ga ababuwa guda biyar da ya kamata ku sani game da Farouk Lawan:

Farkon rayuwarsa

An haifi Farouk Lawan a ranar 6 ga Yulin 1962 a garin Shanono cikin Jihar Kano. Ya girma a Kano inda ya yi karatun firamare da sakandare har ma da gaba da sakandaren a can.

Aikinsa

Ya yi digirinsa na farko a Jami’ar Bayero da ke Kano, indaya fara aiki a zaman Rajistira a Kwalejin Fasaha ta Jihar Kano. Daga baya ya shiga siyasa inda ya yi suna sosai a fagen.

Shekara 16 a matsayin dan majalisa

Ya fara shiga faegen siyasar ne a 1999 lokacin da ya yi takarar kujerar dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Bagwai da Shanono a zauren majalisar tarayya karkashin Jam’iyyar PDP.

Ya kasance a zauren har na tsawon shekara 16 daga 1999 zuwa 2015. Ya sha kaye a karon farko a hannun Sule Aliyu Romo.

Mai Gaskiya/Nagarta

Ko shakka babu Farouk Lawan ya zama wanda muryarsa ta fi amo a zauren majalisar wakilan kafin badakalar da ta shafe shi a 2012.

Ya kasance jarumi marar tsoro wanda ba a nuku-nuku da shi, wadannan sun sanya shi ya samu daukaka a zauren inda aka lakaba masa sunan ‘Mai Gaskiya/Nagarta’.

Ya jagoranci tsige Patricia Etteh

Ya jagoranci gangamin da ya tilasta Kakakin Majalisar mace ta farko, Patricia Eteh, ta yi murabus a 2007. Gungun ’yan majalisar da ya jagoranta ya zargi Eteh da kashe Naira miliyan 620 ba bisa doka ba wajen gyaran gidanta tare da bayar da kwangiloli ga ’yan kanzaginta.

Yadda ya samu kansa a badakalar har ya karkare a fursuna

A 2012, ya shugabanci kwamitin majalisar wanda ya binciki tallafin man da gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayar. An kafa kwamitin bayan zanga-zangar da ta biyo bayan cire tallafin man da gwamnatin Goodluck Jonathan ta yi.

A cikin rahoton kwamitinsa ya ce ya bankado aikata ba daidai ba sosai a harkar tallafin. Rahoton ya ce an biya tallafin Dala miliyan 6.8 na man da ba a ma shigo da shi kasar ba.

Farouk Lawan, ya samu kansa a aikata rashawar ne a yayin da yake bincikar kamfanonin da ake zargin suna da kashi a gindinsu a badakalar tallafin man.

Wani faifan bidiyo ya nuno shi yana karbar Dala 500,000 domin wanke kamfanin Femi Otedolan a cikin rahoton gabanin a gabatar da shi gaban zauren majalisar.

A yayin shari’ar, Otedola ya kafe cewar an kitsa bai wa Lawan rashawar da nufin bankado cin hancin da dan siyasar yake yi kuma da sanin hukumar tsaro ta SSS aka nadi bidiyon. Sai dai shi ma Farouk Lawan din duk da ya yarda ya karbi kudaden amma ya nace kan cewa ya karba ne da niyyar ya kwarmata rashawar da dan kasuwar ya bashi kuma ya tabbatar wa zauren majalisar cewa kwamitinsa ya fuskanci matsin lamba sosai yayin binciken.

Sai dai cikin shekara takwas da ya yi ta kai komo zuwa kotuna daban daban domin wanke kansa, a karshe Mai Shari’ah Angella Otaluka ta same shi da laifuka uku sannan ta yanke masa hukunci ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel