Dan Achaba ya gudu daga asibiti bayan samun labarin matarsa ta haifi ’yan biyu

Dan Achaba ya gudu daga asibiti bayan samun labarin matarsa ta haifi ’yan biyu

  • Mijin ya ce ba zai iya ciyar da koda guda ba ballantana su biyu da mahaifiyarsu
  • Mijin ya tsere ne tun watan Maris kuma har zuwa yau ba a sake jin duriyarsa ba
  • Asibitin na bin matar bashin N131,000 bayan ta iya biyan N30,000

An watsar da wata mata mai suna Abibat Kehinde mai shekara 24, a babban asibitin Epe da ke Legas da nauyin bashin sama da N131,000 da ba a biya ba na kudin magani, wata uku bayan ta haifi tagwaye a asibitin.

Matar ta fada wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Juma’a a Epe cewa mijin nata ya tsere ne bayan ta haihu a ranar 21 ga watan Maris ba tare da ya biya kudin da zai sa a sallame ta daga asibitin ba.

Matar tace:

“Mijina dan Acaba ne.
“Tun bayan da na haifi tagwaye a ranar 21 ga Maris ya bace bat ba a sake jin duriyarsa ba.
"Ban shirya wa sake haihuwar da na biyu ba kafin na samu wannan juna biyun; amma Allah ne mafi sani.

KU KARANTA: Yan sanda sun arce yayin da sojoji suka kutsa caji ofis a Osun

Dan Achaba ya gudu daga asibiti bayan samun labarin matarsa ta haifi ’yan biyu
Dan Achaba ya gudu daga asibiti bayan samun labarin matarsa ta haifi ’yan biyu

DUBA NAN: An rufe yin rijistan Hajjin Bana a Saudiyya, mutum 540,000 suka yi rijista, za'a zabi 60,000

Mahaifiyar tagwayen ta ce ba ta da isasshen abinci da za su ci yayin da jariran kuma suna fama da rashin abubuwan gina jiki tun bayan watsar da ita da mijin ya yi wata uku da suka wuce.

“Mijina ya ce ba zai iya ciyar da da ko da guda ba, barin ma batun ciyar da ’ya’ya biyu tare da mahaifiyarsu. Sannan ya yi korafi game da makudan kudin jinyar da asibitin ke bin mu gabanin ya tsere.
“Tunda lokacin da ya fice daga asibitin, bai sake dawo wa ya duba ni da jariran ba har zuwa yau din nan. Ya bar mu a asibiti sannan ya arce,”

inji Kehinde.

Sai dai ta ce ta yi nasarar biyan N30,000 daga cikin gadon asibitin na N161,000, inda ake bin ta bashin N131,000 da har yanzu ba ta iya biya ba.

Matar ta roki hukumomin asibitin da su sallame ta tare da ’yan tagwayen nata.

Shugabannin Asibitin sun ce sai an biya kashi 90 za'a sallameta

Jami’in kula da jin dadin asibitin na Epe, Ayanbisi Rauf, ya tabbatar da cewa mijin matar ya yi watsi da ita da tagwayen nata.

"Mijin ya yi watsi da ita kimanin wata uku da suka wuce sannan duk kokarin da hukumomin asibitin suka yi domin gano inda yake ya ci tura," inji Rauf.

Ya ce za a sallami mai jegon ne kawai idan ta biya kashi 90 na adadin kudaden da ake bin ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel