Waiwayen Tarihi: Gagarumar gobarar da ta faru a Mina a Hajjin 1997

Waiwayen Tarihi: Gagarumar gobarar da ta faru a Mina a Hajjin 1997

  • Gobarar ta kashe mahajjata kimanin 400 tare da raunata wadansu fiye da 1,500
  • Fashewar tukunyar girki ta gas ce ta haddasa tashin wutar
  • Ta kone tantunan mahajjata kimanin dubu 70 kurmus

Lokacin gudanar da aikin Hajj a ranar 15 ga watan Afrilun 1997, wata gobara mai karfin gaske ta tashi a birnin Mina mai tantuna da ke kusa da Makkah, inda ta hallaka fiye da mahajjata 340 tare da jikkata wadansu fiye da 1,500.

An kiyasta mutum miliyan biyu sun taru a garin na Mina a ranar farko ta aikin Hajjin. Wata tukunyar girki ta gas ce ta yi bindiga da misalin karfe 11:45 na safe na wannan ranar wanda ya haddasa tashin wuta mai karfin gaske a cikin tantunan.

Iskar da gudunta ya kai kilomita 64 cikin sa’a guda ta kara rura wutar ta yadda ba za a iya shawo kanta ba inda ta taimaka wa wutar ta shafi wasu tantunan da ke kusa. An kiyasta tantuna 70,000 ne gobarar ta lakume.

KU KARANTA: Yan sanda sun arce yayin da sojoji suka kutsa caji ofis a Osun

Hajjin 1997
Waiwayen Tarihi: Gagarumar gobarar da ta faru a Mina a Hajjin 1997 Hoto: Haramain Sharifain
Asali: Facebook

DUBA NAN: An rufe yin rijistan Hajjin Bana a Saudiyya, mutum 540,000 suka yi rijista, za'a zabi 60,000

Hukumomin Saudiyyar sun aika da jirage masu saukar ungulu da wasu motocin kashe gobara guda 300 domin kashe wutar. Motocin sun yi ta fesa ruwa da karfin gaske cikin tantunan inda bakin hayaki ya mamaye sararin samaniya, kamar yadda majiyoyin labaran telebijin suka nunar.

Biyo bayan gobarar ta Mina, Sarki Fahd bin Abdulaziz na lokacin a madadinsa kansa da kuma kasar, ya aika da gaisuwar ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu ’yan kasar Saudiyyan da ma ’yan kasashen waje.

Galibin mahajjatan da lamarin ya rutsa da su a cewar jami’an diflomasiyya ’yan kasashen Indiya ne da Pakistan.

Bayan faruwar lamarin, mai lura da Masallatan Biyu masu Tsarki Sarki Fahad (Allah Ya masa rahama) ya bayar da umarnin daukar matakai tare da kare aukuwar hakan a gaba.

Akasarin tantunan da ke Minan an mayar da su wadanda wuta ba za ta iya ci ba tare da samar ingantaccen tsarin kula da gobara.

Tun daga lokacin ba a sake samun aukuwar wata gagarumar gobara ba a wajen, yayin da kananan tashin gobara da ake samu a kan dakile wutar ba tare da ta kashe ko jikkata kowa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel