Ayyuka 774,000: Gwamnatin Tarayya ta umarci bankuna su rika biyan mutane

Ayyuka 774,000: Gwamnatin Tarayya ta umarci bankuna su rika biyan mutane

  • Masu cin gajiyar shirin sun yi zargin babu wanda ya biya ko sisin kwabo
  • Wadanda suka ce an biya su ma sun ce an musu kwange inda aka yanke kudin
  • Yayin da dama har yanzu ba a waiwaye su kan matsayin shirin

Gwamnatin tarayya a ranar Litinin ta umarci bankuna da su hanzarta biyan dukkan mutanen da suke cikin shirinta na fadada ayyuka ga jama’a da ake kira Extended Special Works (ESPW).

Bankunan sun hada da Fidelity da UBA da Heritage da Zenith da Access da FCMB da Yobe Micro Finance.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito a ranar Alhamis, 17 ga Yuni, cewa dubban mutanen da aka dauka a shirin ba a biya su kudinsu ba yayin da wadansu suka ce sau daya kawai aka biya su. Wadansu kuma sun yi zargin cewa an musu kwange a wajen biyan nasu saboda ba a biya su N20,000 ba.

Jami’an Ma’aikatar kwadago ta tarayya da na hukumar samar da ayyukan ta kasa, NDE da bankunan da suke cikin shirin sun hadu a jiya Abuja inda suka yi duba kan rahoton da jaridar Daily Trust din ta yi da ma sauran batutuwan da suka shafi shirin.

Ba su karyata labarin ba kuma a maimakon haka sun ce duk masu ruwa da tsaki suna aiki tukuru domin yi wa tufkar hanci na matsalolin da suka dabaibaiye shirin wanda aka kaddamar da zimmar za a dauki dubban matasa aiki.

KU KARANTA: Dan Achaba ya gudu daga asibiti bayan samun labarin matarsa ta haifi ’yan biyu

Ayyuka 774,000: Gwamnatin Tarayya ta umarci bankuna suna biyan mutane
Ayyuka 774,000: Gwamnatin Tarayya ta umarci bankuna suna biyan mutane
Asali: UGC

KU KARANTA: Waiwayen Tarihi: Gagarumar gobarar da ta faru a Mina a Hajjin 1997

An fara karon farko na shirin tallafawan na watanni uku a ranar 5 ga watan Janairun 2021 kuma ya kare a ranar 5 ga Afrilu.

An tsara shirin ne da zimmar rage radadin COVID-19 ta hanyar samar da ayyuka ga mutum 774,000 a duk fadin kananan hukumomin kasar nan.

Za a biya masu cin gajiyar shirin tallafin N20,000 kowannensu na tsawon watanni uku. Wasu majiyoyin sun ce watakila kudaden ma’aikatan sun kafe ne a hannun wasu bankuna.

Baya ga rashin nasu, Daily Trust ta ruwaito wasu majiyoyin na cewa ba a bai wa wadanda aka dauka su ci gajiyar shirin aiki ba duk da ware Naira biliyan 4 domin samar da wadannan kayayyakin aikin.

Ba a bayyana ainihin adadin da aka fitar don biyan ba yayin da ake zargin aikata ba daidai ba.

Mun fitar da bilyan 26, Festus Keyamo

Da aka tuntube shi a daren jiya, karamin Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Festus Keyamo wanda ke kula da shirin samar da ayyukan, ya ce adadin kudaden da aka fitar kawo yanzu ya kai Naira biliyan 26 duk da cewa wasu kafofin sun ce ya fi haka yawa nesa ba kusa ba.

Ko da a ka tambaye shi ya yi bayanin ina kayayyakin aikin da aka sayo domin shirin suka makale, Keyamo ya ce ba shi da hannu a sayen kayayyakin kuma ya nemi dan jaridar da ya tuntubi hukumar ta NDE.

Da aka tuntube shi, Darakta Janal na hukumar ta NDE Malam Nuhu Fikpo, ya nemi dan jaridar da ya neme shi a ofishinsa yau Talata domin samun cikakken bayanin adadin kudaden da gwamnatin tarayyar ta sake da adadin abin da hukumar ta biya masu cin gajiyar shirin ya zuwa yanzu da ma abin da aka kashe wajen sayan kayayyakin aikin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel