2023: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya bayyana yadda magajin Buhari zai Fito

2023: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya bayyana yadda magajin Buhari zai Fito

  • Wani tsohon sanata a tarayyar Najeriya, Olabiyi Durojaiye, ya yi kira da a karfafa harkokin tsaro a kasar
  • Durojaiye ya bayyana cewa mai yiwuwa ba za a gudanar da babban zaben 2023 ba idan hadin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar na fuskantar barazana
  • A cewarsa, ya zama dole 'yan Najeriya su zabi tsakanin shugaban jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu da sauransu

Olabiyi Durojaiye, tsohon dan takarar shugaban kasa kuma sanata a jamhuriya ta hudu, ya ce nan ba da jimawa ba ‘yan Najeriya za su zabi wanda zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.

A wata hira ta musamman da ya yi da jaridar The Punch, tsohon sanatan ya lura cewa dole ne kasar ta daidaita kafin ayi magana game da babban zaben da ke tafe.

KU KARANTA KUMA: Da Duminsa: Masu zanga-zangar 'Buhari Must Go' sun banka wuta a hanyar zuwa filin tashin jirage na Abuja

2023: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya bayyana yadda magajin Buhari zai Fito
Sanata Durojaiye ya yi kira ga hadin kan kasar Hoto: Legit.ng

Legit.ng ta tattaro cewa dole ne gwamnatin tarayya ta tabbatar akwai kundin tsarin mulki wanda zai yi aiki kuma karbabbe ga mutane.

Da yake magana kan zargin tsayawar shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) takara, Durojaiye ya lura cewa tsohon gwamnan na jihar Lagas na da gogewar da zai jagoranci Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya sassauta, ya amince zai tattauna da 'yan kudu maso gabas kan rabewa

Ya ce:

"Idan muka zo zaben, Asiwaju mutum ne mai matukar gogewa, irin wanda zai iya tsayawa takarar shugaban kasa a kowace kasa. Akwai wasu ma da zasu zo kuma mutane zasu zabi wanda suka fi so. Za su kalli asali da tushensu."

Babu wata kabila da za ta ware saura

Tsohon sanatan ya bayyana cewa ya kamata wadanda ke ganin cewa kasar mallakar wasu kebantattun aji ne su koyi darasin cewa ba za su iya rike shi na tsawon lokaci ba.

Ya kara da cewa matasa za su samu kwarin gwiwa da karfin zuciya a kan makomarsu, ya kara da cewa da alama ba su da karfin zuciya.

Durojaiye ya kara cewa:

"Yawancin abubuwan da suke a matakin tarayya ya kamata a kara su sannan kuma idan muka yi zaɓe, zai tafi yadda ya kamata. Zamu samu damar ɗaukar gogaggun yan takara a wannan lokacin. Ba mu san yawan wadanda za su fito ba tukuna. Amma ba ni da wani mugun nufi kan Asiwaju."

Ba zai yiwa ba: Shugaba Buhari ya ce ba ga kowane dan siyasa zai mika mulki ba

A gefe guda, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ya ce ba zai mika mulki ga ‘yan siyasar da ba za su iya cin zabe a yankunansu ba, ya kara da cewa babu wani abu da kasar nan ke bukata a yanzu sama da zaman lafiya.

Don haka, ya ce kasar za ta fi kyau idan ta ci gaba da kasancewa dunkulalliya a matsayin kasa mai cikakken iko fiye da rarrabuwa zuwa bangarori, Vanguard ta ruwaito.

Shugaba Buhari na magana ne a matsayin bako na Musamman na girmamawa a wajen kaddamar da Kudirat Abiola Sabon Gari, Gidauniyar Zaman Lafiya ta Zaria da aka gudanar a Otal din Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a jiya Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel