Ba zai yiwa ba: Shugaba Buhari ya ce ba ga kowane dan siyasa zai mika mulki ba

Ba zai yiwa ba: Shugaba Buhari ya ce ba ga kowane dan siyasa zai mika mulki ba

  • Shugaba Buhari ya sake jaddada cewa ba ga kowa zai amince ya mika mulki ba a kasar
  • Ya kuma bayyana cewa, wasu 'yan Najeriya basu san illar son raba kasar da suke nema ba
  • Ya bayyana haka ne a Zaria, jihar Kaduna a jiya Asabar yayin da ya samu wakilcin wani jami'i

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ya ce ba zai mika mulki ga ‘yan siyasar da ba za su iya cin zabe a yankunansu ba, ya kara da cewa babu wani abu da kasar nan ke bukata a yanzu sama da zaman lafiya.

Don haka, ya ce kasar za ta fi kyau idan ta ci gaba da kasancewa dunkulalliya a matsayin kasa mai cikakken iko fiye da rarrabuwa zuwa bangarori, Vanguard ta ruwaito.

Shugaba Buhari na magana ne a matsayin bako na Musamman na girmamawa a wajen kaddamar da Kudirat Abiola Sabon Gari, Gidauniyar Zaman Lafiya ta Zaria da aka gudanar a Otal din Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a jiya Asabar.

KU KARANTA: Mu Tagwaye Ne: Koriya Ta Arewa Na Bukatar Kara Dankon Alaka da Najeriya

Shugaba Buhari ya sake jaddada cewa, ba ga kowa zai amince ya mika mulki ba
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shugaban ya ci gaba da cewa wadanda ke neman raba kasar ba su san yaki da illar sa ba. Shugaba Buhari wanda ya samu wakilcin Babban Sakatare, Raya Kudaden kasa, Alhaji Mohammed Bello Shehu, ya kara bayyana cewa raba kasar ba zai taimakawa batutuwa da dama a kasar ba.

A cewarsa:

"Kira na ga kowa a nan shi ne, ya yi kokari ya ilimantar da ’ya’yansa. Mun fi kyau a matsayinmu na kasa daya, babu yadda za a yi mu rabu, rabuwar kasar ba zai taimaka ba.”

Shima da yake jawabi, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai, wanda ya sami wakilcin Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr Shehu Usman Mohammed, ya yi gargadin cewa kasar a bar kasar ta ci gaba da kasacewa a hade fiye da rabuwa, yana mai cewa dole ne mu jure wa zama tare.

Ya yi nuni da cewa, masu kiran a raba kasar ya kamata su dawo cikin hayyacinsu saboda 'yan Najeriya yanzu suna rayuwa a kowane bangare na kasar, inji rahoton Sun News.

KU KARANTA: An Kame Buhunnan Kudi da Aka Shigo Dasu Daga Kasar Waje a Filin Jirgin Jihar Kano

Minista Ya Bayyana Yadda ’Yan Najeriya Ke Kokarin Tura Buhari Ga Halaka

A wani labarin, Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Dakta Chris Ngige ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya jure da yawa daga masu sukarsa, yana mai sake jaddada cewa ‘yan Najeriya da dama na son kure shi (Buhari) fiye da yadda ya kamata.

Ngige ya yi magana ne lokacin wata tattaunawa da Channels Tv a cikin shirin News Night wanda aka watsa a ranar Litinin kuma Legit.ng Hausa ta samo, inda ya bayyana cewa shugabanni da yawa ba za su amince da irin sukar da Buhari ke fuskanta ba.

"Shin Shugaba Obasanjo zai iya baku damar irin wannan hali?… Ba zai bar ku haka ba! Don haka, wannan shugaban (Buhari) doki ne mai gudun tsiratarwa amma ku (‘yan Najeriya) kuna son ingiza shi ya mutu,” in ji Ngige yayin tattaunawar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel