Dalibin makarantar Kebbi ya mutu sakamakon musayar wuta tsakanin sojoji da masu garkuwa

Dalibin makarantar Kebbi ya mutu sakamakon musayar wuta tsakanin sojoji da masu garkuwa

  • Dalibi guda daya cikin wadanda aka sace daga makarantar FGC Birnin Yauri, Jihar Kebbi ya mutu
  • Dalibin ya mutu ne sakamakon musayar wuta da jami'an tsaro suka yi da yan bindigan a safiyar ranar Juma'a
  • Mataimakin kwamandan rundunar hadin gwiwa na yankin arewa maso yamma Abubakar Abdulkadir ya tabbatar da haka

Daya daga cikin daliban da yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai makarantar sakandare na gwamnatin tarayya da ke Birnin-Yauri a jihar Kebbi ya riga mu gidan gaskiya.

The Cable ta ruwaito cewa Abubakar Abdulkadir, mataimakin kwamandan rundunar hadin gwiwa a arewa maso yamma ne ya sanarwa manema labarai hakan a ranar Juma'a.

Daliban FGC Birnin Yauri, Jihar Kebbi
Daliban FGC Birnin-Yauri, Jihar Kebbi. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe ɗan sanda, sun sace 'yan ƙasar waje da ke aikin layin dogo na Legas zuwa Ibadan

Kawo yanzu ba a tantance adadin daliban da yan bindigan suka sace ba yayin harin da suka kai a ranar Alhamis.

Sai dai, wasu kafafen watsa labarai a Nigeria sun bayyana cewa dalibai 30 ne aka sace.

Abdulkadir ya ce sojojin sun yi musayar wuta da masu garkuwar a ranar Juma'a, hakan ya tilasta su sakin mutane biyar cikin wadanda suka sace kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

"A safiyar yau mun yi arangama da masu garkuwar. Sun taho wurin da muka kafa shinge, sai muka yi musayar wuta da su," in ji shi.
"A lokacin, sun saki biyar cikin daliban da malama guda daya. Amma abin bakin ciki ina ganin mun rasa daya daga cikin daliban."

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: 'Yan bindigan da suka kai hari Makarantar Kebbi sun harbi ɗalibai biyu, Shaida

Wannan shine satar dalibai na baya-baya cikin wadanda aka rika kai wa a makarantun arewacin Nigeria.

A kalla dalibai 700 ne aka sace a hare-haren tun Disambar 2020.

Bana tunanin ƴan bindigan da suka kai hari makarantan mu ƴan Nigeria ne, Ɗaliban Kebbi

Wata daliban makarantar FGC Birnin-Yauri a jihar Kebbi wacce ta tsira daga harin a ranar Alhamis ta ce bata tunanin yan bindigan da suka kai hari makarantansu yan Nigeria ne, The Cable ta ruwaito.

A ranar, Alhamis ne yan bindiga suka kutsa makarantar a kan babura suka kuma yi awon gaba da malamai da dalibai da dama.

Yayin harin, yan sanda da ke makarantar sun yi kokarin dakile harin amma yan bindigan sun fi su yawa hakan ya yi sanadin rasuwar jami'in dan sanda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel