Da dumi: An ayyana Raisi mai ra’ayin rikau a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban Kasar Iran

Da dumi: An ayyana Raisi mai ra’ayin rikau a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban Kasar Iran

  • Zababben Shugaban Kasar Ebrahim Raisi mai ra’ayin mazan jiya ne kuma shugaban bangaren shari’ar Iran a yanzu
  • Ya samu fiye da kashi 60 na kuri’un da aka kada
  • Yana cikin jerin jami’an gwamnatin Iran da Amurka ta kakabawa takunkumi

Dan ra’ayin rikau din nan kuma jagoran sashen shari’a a zaben Shugaban Kasar Iran Ebrahim Raisi ya lashe zaben shugaban kasar inda zai zama shugaban kasar na takwas, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta sanar.

Ma’aikatar wajen a ranar Asabar ta tabbatar da Raisi ya samu kashi 61.95 na kuri’un da aka kada a zaben ranar Juma’ah inda aka samu masu jefa kuri’a kashi 48.8 wanda shi ne mafi karanci tun bayan juyin juya halin shekarar 1979, rahoton Aljazeera.

Raisi ya samu kuri’a 28,933,004.

DUBA NAN: Ya kamata a kara farashin wutan lantarki a Najeriya, yayi arha da yawa: Bankin Duniya

Raisinya ci zabe
Da dumi: An ayyana Raisi mai ra’ayin rikau a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban Kasar Iran Hoto:AFP
Asali: UGC

KU KARANTA: Na gina gida da daukar nauyin ‘ya’yana 15 - Dattijon da ya shekara 51 yana sana'ar sayar da jarida

Sakamakon zaben

Tsohon kwamandan Askarawan Juyin Juya Halin kasar Mohsen Rezaei ya zo na uku da kuri’a 3,412,712 inda dan takara mai matsakaicin ra’ayin rikau Abdolnasswer Hemmati ya biyo bayansa da kuri’a 2,427, 201, sannan mai tsaurin ra’ayin mazan jiya Amir Hossein Ghazizadeh Hashemi ya samu kuri’a 999,718.

“Babu wani abu na aikata ba daidai ba da aka fuskanta da zai shafi ingancin sakamakon zaben,” inji Ministan cikin gidan Iran Abdolreza Rahmani-Fazli yayin taron manema labarai a Tehran.

Dan takara Rezaei da Hemmati da Hashemi tun farko sun amince da shan kaye gabanin sanar da sakamakon zaben a hukumance ranar Asabar.

Raisi zai karbi mulki a watan Agusta daga hannun mai matsakaicin ra’ayin rikau Shugaba Hassan Rouhani wanda tsarin mulkin kasar bai ba shi damar sake tsayawa takarar karo na uku.

Raisi zai zama Shugaban Kasar Iran na farko da Amurka ta sanya wa takunkumi tun gabanin ya hau mulki duba da tun a shekarar 2019 Amurkar ta saka sunansa a jerin jami’an kasar da ta kakaba wa takunkumi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel