Zan mayar muku da kudinku na taimako idan kuna aikata sabo: Fasto ya ja kunnen mabiya cocinsa

Zan mayar muku da kudinku na taimako idan kuna aikata sabo: Fasto ya ja kunnen mabiya cocinsa

  • Fasto Kumuyi na majami’ar Deeper Life ya yi wa’azi kan bayar da taimako daga dukiyar haram, yana cewa ba a karbar wannan taimakon
  • Ya ce zai mayar wa mabiya cocinsa kudi da sauran kyautukan da tushense haram ne
  • A cewarsa, rayuwa cikin yardar Allah ta fi muhimmanci kan taimaka wa cocin

Babban limamin kuma wanda ya kafa majami’ar nan ta Deeper Christian Life Ministry, Fasto Williams Folorunsho Kumuyi, ya ce zai maida wa duk wani mamban cocinsa da kudi ko wata kyautar da ya yi masa idan dai ta hanyar haram ya samo dukiyar.

Jaridar Sahara Reporters da ake wallafa wa ta intanet ta ruwaito Faston yana cewa zai aikata hakan idan ya gano mabiyin cocin nasa yana rayuwa cikin aikata sabo.

Ya bayyana hakan ne a helkwatar majami’ar da ke a Legas lokacin da yake magana ga mabiya cocin nasa.

KU KARANTA: Na gina gida da daukar nauyin ‘ya’yana 15 - Dattijon da ya shekara 51 yana sana'ar sayar da jarida

Fasto kumuyi yayi zafi
Zan mayar muku da kudin taimako idan kuna aikata sabo: Fasto ya ja kunnen mabiya cocinsa Hoto: The Nation
Asali: UGC

DUBA NAN: Ya kamata a kara farashin wutan lantarki a Najeriya, yayi arha da yawa: Bankin Duniya

Kuna barnata kudinku ne kawai

Ya kara da cewa wadanda ke taimaka wa cocin amma suke rayuwa cikin aikin sabo suna barnata da dukiyoyin da suke tallafa wa cocin ne kawai, kamar yadda jaridar, Daily Post ta ruwaito.

Ya ce Allah ba Ya son dukiyar mai aikin sabo yana mai jaddada kiran mutane da su rika rayuwa cikin kyautata tsakaninsu da Mahaliccinsu.

Ya ce idan akwai wanda ya san masu sabon Allah a cocinsa ya kuma san adadin abin da suka taimaka wa cocin da shi, to a shirye yake da ya zaftare kudaden Nasiru ya mayar musu da kudaden saboda Allah ba Ya bukatar su.

Kana cikin la’ana idan ba ka bada taimakon majami’a

A daya gefen kuma kafar labarai ta Legit.ng tun da farko ta ruwaito wani mai wa’azin Kirista a Najeriya Fasto David Oyedepo, ya wallafa ra’ayinsa game da bayar da taimako ga majami’a a shafinsa na Twitter

Malamin addinin Kiristan ya ce bada kudin taimakon cocin wani wajibin al’amari ne da ba wanda zai guje masa.

Ya ci gaba da cewa arziki da ci gaban mutum ba sa samuwa sai idan mutum yana bada taimakon majami’a

A cewarsa, duk wanda bai bada kudin taimakon ba to kwana da sanin cewa yana cikin la’antar arziki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel