Gwamna Nasir El-Rufai ya kori masu mukaman siyasa 99 a Kaduna

Gwamna Nasir El-Rufai ya kori masu mukaman siyasa 99 a Kaduna

  • Gwamna El-Rufa'i ya ce za a ci gaba da rage adadin ma’aikatan
  • Ya nunar da cewa dole ce ta sa gwamnatin sallamar ma’aikatan saboda raguwar kudaden da jihar ke samu daga tarayya
  • Ya tabbatar wa ma’aikatan gwamnatin jihar za ta ci gaba da biyan mafi karancin albashin N30,000

Gwamnan Jihar Kaduna ya ce gwamnatin jihar ta fara aiwatar da tsarin garambawul na ma’aikatan jihar ta hanyar korar masu rike da mukaman siyasa 99.

Sai dai ya ce har yanzu fa gwamnatin jihar ba ta riga ta sallami kowane ma’aikaci ba kawai ma’aikatun gwamnatin da ke da nasaba da kananan hukumomi ne kadai suka sallami ma’aikatan.

Gwamnan wanda ya yi manema labarai bayanin hakan a ranar Alhamis ya ce wadanda aka kora daga bakin aikin sun hada da ma’aikatan kananan hukumomin jihar 23 da masu aiki a hukumar bayar da ilimin bai daya ta jihar (SUBEB) da ma’aikatan kiwon lafiya a matakin farko.

Ya nunar da cewa masu rike da mukaman siyasan da aka sallaman sun kai kashi 30 na adadin masu rike da mukaman siyasar a jihar.

A cewar El-Rufai

’Ya zuwa yanzu masu rike da mukaman siyasa 99 ne suka rasa ayyukansu, amma har yanzu ba mu fara rage ma’aikatan gwamnatin jihar ba tukuna.
“Muna so mu yi wa ma’aikatan adalci ne. Da farko mun yi alkawarin cewa kafin mu rage ma’aikatan jihar sai mun fara da masu rike da mukaman siyasa tukuna,”

DUBA NAN: Ya kamata a kara farashin wutan lantarki a Najeriya, yayi arha da yawa: Bankin Duniya

Gwamna Nasir El-Rufai ya kori masu mukaman siyasa 99 a Kaduna
Gwamna Nasir El-Rufai ya kori masu mukaman siyasa 99 a Kaduna
Asali: Facebook

KU KARANTA: Na gina gida da daukar nauyin ‘ya’yana 15 - Dattijon da ya shekara 51 yana sana'ar sayar da jarida

Gwamnan ya kara da cewa dole ne a ci gaba da rage ma’aikatan kamar yadda aka tsara sakamakon kason da jihar ke samu daga rabon arzikin tarayya ya yi kasa.

Ya karyata batun da ake yada wa cewa albashin masu rike da mukaman siyasa ne ke cinye kusan kudin da jihar ke samu.

“A watan Maris din nan, albashin masu rike da mukaman siyasar ya kai Naira miliyan 259 yayin da na ma’aikatan ya kai Naira biliyan 3.13, ban da kudaden da gwamnatin ke bayar wa a matsayin gudummawar tara kudaden fansho da sauran harkokin gudanarwa,” inji Gwamnan.

Ya yi alkwarin cewa gwamnatin jihar ba za ta daina biyan mafi karancin albashin Naira dubu 30 da ta fara aiwatar wa.

A bangare guda, gwamna Nasir Ahmed El-Rufai na jihar Kaduna, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta tsani ko ta bi wadanda ke yi mata bita-da-kulli da sharri ba.

El- Rufai ya ce iyakar abunda za su yi shine hada duk masu yi musu hakan da Allah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel