Na kan yi sallah raka’a 2 a daren Alhamis sai na hada masu yi mana sharri da Allah – El-rufai

Na kan yi sallah raka’a 2 a daren Alhamis sai na hada masu yi mana sharri da Allah – El-rufai

  • Gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya ce ba zai nufi masu yi masu bita-da-kulli da sharri ba
  • El-Rufai ya ce iyakacin abun da ya kan yi shine yin sallah raka'a biyu a daren ranar Alhamis sannan ya kai kararsu gaban Allah
  • Ya kuma yi albishir da cewa da zaran an kammala tantancewa ma’aikata za a koma jin dadi da samun albashi a bisa kan lokaci a jihar

Gwamna Nasir Ahmed El-Rufai na jihar Kaduna, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta tsani ko ta bi wadanda ke yi mata bita-da-kulli da sharri ba.

El- Rufai ya ce iyakar abunda za su yi shine hada duk masu yi musu hakan da Allah, sashin Hausa na Premium Times ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Tauraron kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ya auri shahararriyar jarumar fina-finan Hausa

Na kan yi sallah raka’a 2 a daren Alhamis sai na hada masu yi mana sharri da Allah – El-rufai
Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna Hoto: Lawcare Nigeria
Asali: UGC

Ya ce:

“Duk wanda ya yi mana kazafi, saboda wata mugun kudirinsa, ba za mu bishi da sharri ba ko kuma mu tsangwame shi, iyaka in tashi cikin dare ranar Alhamis in yi raka’a biyu in hada shi da Allah.”

Gwamnan ya ci gaba da yin karin haske kan cewa wasu ma’aikatan da ake biyansu rabin albashi, cewa an samu wasu ma’aikata fiye da 9000 da matsaloli a takardunsu ko asusun ajiyarsu.

Ya kara da cewa da zaran an kammala tantancewa ma’aikata za a ji dadin gwamnatinsa tare da samun albashi a bisa kan lokaci.

Kan zanga-zangar kungiyar kwadago suka yi, El-Rufai yace kudi aka basu su zo su tada hankalin mutanen Kaduna.

KU KARANTA KUMA: Alhaji Ibrahim Mohammed: Ku sadu da Sarkin makafi a Ibadan wanda ke da mata 3 da yara da yawa

“Kungiyar kwadago sun zo Kaduna ne saboda sun ci kudin wasu kuma dole sai sun yi yajin aikin. Gwamnatin Tarayya ta kasa hukunta kungiyar, amma kuma mu sai mun bi wa mutane hakkokinsu saboda tun farko sun ketare doka ne.
“Dalilan da NLC suka fadi karya ne. Idan NLC suka dawo Kaduna sai sun dandana kudar su.”

Wanda zai gaje ni sai yayi rusau da ragargazar gidaje fiye da ni, El-Rufai

A gefe guda, Gwamna El-Rufai ya ce wanda zai gaje shi zai rufe gidaje tare da ragargajesu domin habaka jihar fiye da yadda yayi a jihar.

Ya ce wasu jama'a na kallonsa a mai rusau kuma sun kosa wa'adin mulkinsa ya kare, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan wanda ya sanar da hakan a wata tattaunawa da aka yi da shi a gidajen rediyo a ranar Alhamis, ya ce mazauna jihar yanzu suna jinjina masa a kan yadda mulkinsa ke gyara birane,

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng