Masar ta tabbatar da hukuncin kisa kan Shehunnai yan kungiyar Ikhwan 12

Masar ta tabbatar da hukuncin kisa kan Shehunnai yan kungiyar Ikhwan 12

  • Kotun ta same su da laifuka daban daban a loakcin zaman dirshen 2013
  • Cikin lafukan har da kashe jami’an ’yan sanda da lalata kadarorin gwamnati
  • Idan Shugaban Kasar ya sanya hannu kan hukuncin za a zartar musu da hukuncin

A ranar Litinin babbar kotun farar hula a Masar ta tabbatar da hukuncin kisa kan mambobin kungiyar ‘Yan Uwa Musulmi 12, wanda hakan ya kawo karshen shari’ar da ke da nasaba da kisan daruruwan mutane da jami’an tsaro suka yi a 2013, a cewar majiyoyin shari’ar kasar, rahoton Reuters.

Hukuncin wanda ba za a iya daukaka kara a kansa ba, yana nufin mutum 12 da aka yanke hukuncin a kansu za a iya zartar da hukuncin kisan a kansu da zarar Shugaban Kasa Abdel Fattah el-Sisi ya rattaba hannu a kan hukuncin.

AlJazeera a ruwaito cewa mutanen sun hada da Abdul Rahman Al-Bar, da aka fi sani da babban malamin kungiyar mai fatawa da Mohamed El-Beltagi, wani tsohon dan majalisar kasar da Osama Yassin, tsohon ministan kasar.

KU KARANTA: Alheri kan alheri: Ma’aurata ’yan Najeriya sun samu ’yan biyu shekara 21 suna jiran haihuwa

Shehunnai yan kungiyar Ikhwan 12
Masar ta tabbatar da hukuncin kisa kan Shehunnai yan kungiyar Ikhwan 12, Malaman Duniya sun yi ca Hoto: www.aljazeera.com
Asali: UGC

KU DUBA: Ana mini barazanar kisa, Shugaban Hukumar EFCC Abdulrashid Bawa

An fara damke mambobin Ikhwan tun bayan juyin mulkin da aka yiwa Mursi

Mambobin kungiyar da dama ne aka yanke wa hukuncin kisa a wasu shari’o’in da ke da nasaba da tashin hankalin da ya biyo bayan sojoji suka hambare gwamnatin da dan kungiyar ta ‘Yan Uwa Musulmi wato Shugaban Kasa Mohamed Morsi a 2013, amma wata kotun musamman ta umarci a sake musu shari’ah.

Biyo bayan hambare Morsi a watan Yulin 2013 a daidai lokacin da ake kazamar zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatinsa, magoya bayansa na kungiyar ta ‘Yan Uwa Musulmi sun yi zaman dirshen Dandalin Rabaa Al-Adawiya da ke gabashin Alkahira suna neman a dawo da shi kan karagar mulki.

Wata guda bayan hambar da shi, jami’an tsaro sun dirar wa dandalin inda suka kashe mutum kimanin 800 a rana guda.

Hukumomin kasar a lokacin sun ce masu zaman dirshen suna dauke ne da makamai kuma an dauki matakin murkushe su ne da zimmar tarwatsa su tare da yaki da ta’addanci.

Farmakin ya bude kofar dirar wa ‘yan adawar kasar Masar da hukumomin kasar suka rika yi na tsawon lokaci.

Wadanda aka yanke wa hukuncin kisan a ranar Litinin din an same su ne da laifin bada makamai ga gungun miyagun da suka rika kai hare-hare kan jama’a da jami’an ‘yan sanda tare da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, a cewar kotun a cikin hukuncin da ta yanke.

Sauran tuhume-tuhumen sun hada da kashe ‘yan sanda da bijirewa hukuma tare da mamaya da lalata kadarorin gwamnati.

Sannan a daya gefen, kotun ta rage hukuncin wadansu mutum 31 mambobin kungiyar ta ’Yan Uwa Musulmi, kamar yadda wani jami’I ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarn AFP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel